Ana tuhumar magidanci da leken matar aure tana wanka
An gurfanar da wani magidanci mai suna Ibrahim M. Gezawa a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke Fagge a birnin Kano bisa zarginsa da laifin leka wata matar aure a lokacin da take wanka a ban-daki. Matar mai suna Usaina Mohammed ta shaida wa kotun cewa mutumin ne wanda suke zaune gida daya, ya yi […]
An gurfanar da wani magidanci mai suna Ibrahim M. Gezawa a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke Fagge a birnin Kano bisa zarginsa da laifin leka wata matar aure a lokacin da take wanka a ban-daki.
Matar mai suna Usaina Mohammed ta shaida wa kotun cewa mutumin ne wanda suke zaune gida daya, ya yi wa kofar ban-dakin gidan hudoji masu yawa inda yake amfani da hudojin wajen leka ta a ban-daki a duk lokacin da take wanka.
“Ran nan ina wanka sai na kula cewa hudojin kofar ban-dakin da nake ciki sun yi yawa. ina kallon wata huda a jikin kofar sai muka yi ido biyu da wannan mutum da muke haya gida daya da shi. Ban san iya lokacin da ya dauka yana leka ni a ban-daki ba a zaman da muka yi na shekara daya da rabi tare,” inji ta.
Sai dai a nasa banagren wanda ake zargin ya musanta laifin da ake zarginsa da shi inda ya ce sharri matar take yi masa, domin dama haka kofar ban-dakin gidan take da hudoji a jikinta, kuma a cewarsa wata matar da ta zauna a gidan za ta iya yin shaida a kan haka.
Alkalin Kotun Mai shari’a Ali Wudilawa ya dage shari’ar zuwa mako daya inda ya umarci ’yan sanda su kara bincike a kan lamarin.
A wani labarin ’yan sanda sun kama wani dan kwana-kwana a Kano bisa zarginsa da laifin boyewa tare da yi wa wata yarinya ’yar kimanin shekara takwas fyade.
dan kwana-kwanan Umar Mohammed da abokin aikinsa Mustapha Idris da ya gudu suna aiki ne a ofishin hukumar da ke Sharada, kuma an ce sun dauki yarinyar ce da aka boye sunanta zuwa Kunbotso suka rika lalata da ita.
Kakakin ’Yan sandan Jihar Kano ASP Magaji Musa Majiya ya ce, “Bayan sun boye yarinyar a ranar 20 ga Mayu tare da lalata da ita, sai suka nemi kudin fansa Naira miliyan daya daga mahaifinta. Mun kama Umar Mohammed kuma za mu ci gaba da neman abokin aika-aikarsa don su fukanci hukunci.” Ya ce sun rubuta takarda ga Hukumar Kwana-Kwana kan ta taimaka wajen kamo daya ma’aikacin da ya gudu .
Umar Mohamamed ya yi ikirin yin lalata da yarinyar, sai dai ya shaida wa Aminiya cewa, sau biyu kawai ya kwanta da ita ba da yawa ba kamar yadda ake fadi.
Lokacin da Aminiya ta tuntubi Kwamandan Hukumar Kwana-Kwana Alhaji Balarabe Kabara ya ce “Na riga na dakatar da wanda ake zargi daga aiki zuwa lokacin da za a gama bincike. Idan an kama shi da laifi dokar ladabtarwa za ta yi aiki a kansa don ya zama darasi ga saura.”