Ana tuhumar magidanci da yi wa diyarsa ciki a Ibadan
A ranar Litinin mai zuwa ce kotun Majistare da ke Iyaganku a Ibadan, za ta ci gaba da sauraron shari’ar wani mutum mai suna Ahmed Akintola, mai shekaru 45 wanda ’yan sanda suka gurfanar bisa zargin yi wa diyarsa fyade, wadda a yanzu haka take dauke da cikin wata uku.Lokacin da aka gabatar da shi […]

A ranar Litinin mai zuwa ce kotun Majistare da ke Iyaganku a Ibadan, za ta ci gaba da sauraron shari’ar wani mutum mai suna Ahmed Akintola, mai shekaru 45 wanda ’yan sanda suka gurfanar bisa zargin yi wa diyarsa fyade, wadda a yanzu haka take dauke da cikin wata uku.
Lokacin da aka gabatar da shi gaban kotun a cikin makon jiya, Alkalin kotun, mai shari’a Kehinde Durosaro-Tijani, ta ce a garkame wannan mutumi a gidan yari na Agodi a Ibadan har zuwa ranar Litinin da za ta ci gaba da sauraron karar.
Mai gabatar da kara, Mista Oluyemi Eyiarami, ya shaida wa kotun cewa, wanda ake tuhuma, ya tilasta yin lalata da diyarsa (an sakaya sunanta) ’yar shekara 16 da haihuwa, wadda yanzu haka take dauke da juna biyu na wata uku. Ya ce, yarinyar ta tabbatar da cewa a cikin dare mahaifin nata ya sha saukowa daga kan gado yana yin lalata da ita a kan tabarmar da take kwance a cikin daki daya da suke kwana (da shi mai gida da matarsa da ’ya’yansa).
Wannan yarinya ta ce ta kai karar mahaifin nata ga dangin mahaifiyarta, amma babu wani taimako da suka yi domin hana shi saduwa da ita har zuwa lokacin da al’adarta ta dauke.
Saboda haka mai gabatar da karar ya nemi kotun ta yi wa Ahmed Akintola hukunci mai tsanani da zai zama darasi ga masu sha’awar aikata irin wannan mummunan aiki, wanda ya saba wa sashi na 357 da 358 na kundin dokar laifuka na Jihar Oyo na shekara ta 2000.
Kamar yadda wakilinmu ya ruwaito, a lokacin da mai gabatar da karar yake karanta tuhumar da ake yi wa Ahmed Akintola, ya yi shiru ba tare da cewa uffan ba, kuma babu wani lauya da ya yi kokarin kare shi a wannan rana. A binciken da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa, zai yi wuya kotun ta iya yanke wani hukumci a yanzu da wannan yarinya take dauke da ciki na wata uku, sai bayan ta haihu sannan ne za a iya tabbatar da gaskiyar aukuwar wannan al’amari ta hanyar gwajin jini daga asibiti. Idan kuma ya amsa laifinsa maganar ta zo karshe ke nan.