Ana tuhumar magidanci da yi wa yarinya fyade a Bayelsa
Wani magidanci mai shekara 40 (an sakaya sunansa) ya yi wa wata yarinya ’yar shekara hudu da haihuwa fyade a Jihar Bayelsa.Wannan lamari ya faru ne a karamar Hukumar Ijaw ta Kudu. Shugabar kungiyar Yaki da Cin zarafin Yara, Uwargida Mariam Kombo-eze ce ta tabbatar da haka a wani taron gangami da aka shirya, wanda […]
Wani magidanci mai shekara 40 (an sakaya sunansa) ya yi wa wata yarinya ’yar shekara hudu da haihuwa fyade a Jihar Bayelsa.
Wannan lamari ya faru ne a karamar Hukumar Ijaw ta Kudu. Shugabar kungiyar Yaki da Cin zarafin Yara, Uwargida Mariam Kombo-eze ce ta tabbatar da haka a wani taron gangami da aka shirya, wanda ya samu halartar wakilan Asusun Yara na Majalisar dinkin Duniya (UNICEF).
Haka nan kuma Uwargida Kombo-eze ta bayyana karuwar matsalar fyade a Bayelsa, inda ta kara bayyana cewa wasu yara biyu su ma an ci zarafinsu a jihar, ciki har da wata yarinya mai shekara bakwai; wadda sanadin fyaden ta rasa ranta sakamakon harbinta da cutar kanjamau da mai fyden ya yi.
A cewarta: “Wannan lamari abin takaici ne, don haka za mu bukaci Majalisar Dokokin Jihar Bayelsa ta kafa dokar hana cin zarafin yara kanana.”
Wata majiya da ta bukaci sakaya sunanta ta shaida wa Aminiya cewa masu yi wa kananan yara fyade, bokaye da matsafa ne ke gaya musu karya cewa idan sun yi wa kananan yara mata fyade za su warke daga cutar kanjamau da suke dauke da ita.