Ana tuhumar magidanci da yin ciki ga budurwa bebiya a Kano..1
Wani magidanci mai shekara 38 ya gurfana a gaban Kotun Shari’ar Musulunci ta ’Yan Alluna da ke Fagge bisa zargin yi wa wata bebiya ’yar shekara 16 ciki. dan sanda mai gabatar da kara Ahmad Musa ya bayyana wa kotu cewa wanda ake zargin mai suna Idi Wanzam mazaunin Unguwar Sheka ya yi lalata da […]
Wani magidanci mai shekara 38 ya gurfana a gaban Kotun Shari’ar Musulunci ta ’Yan Alluna da ke Fagge bisa zargin yi wa wata bebiya ’yar shekara 16 ciki.
dan sanda mai gabatar da kara Ahmad Musa ya bayyana wa kotu cewa wanda ake zargin mai suna Idi Wanzam mazaunin Unguwar Sheka ya yi lalata da bebiyar (an sakaya sunata) sau biyu lamarin da ya sa ta samu juna biyu. Ya ce ana zargin Idi Wanzam mazaunin Unguwar Sheka da lalata da bebeyar ne a lokacin da ta je gidansa dibar ruwa.
Da take bayyana wa kotu yadda lamarin ya faru ta hanyar mai fassara bebiyar ta ce kimanin wata shida da suka wuce wanda ake zargin ya yi lalata da ita sau biyu a lokacin da aka aike ta gidansa dibar ruwa.
Mai gabatar da kara ya ce laifin ya saba wa sashi na 126 na Final Kod na shekarar 2000.
Da alkalin kotun Mai shari’a Abubakar Ayagi ya waiwayi wanda ake zargin wanda ke da ’ya’ya hudu ya amsa laifinsa nan take. Sai alkalin ya dage shari’ar zuwa ranar 28 ga Nuwamba, inda ya ce a ci gaba da tsare wanda ake zargi a gidan kurkuku.