Ana tuhumar mahaifi da matarsa bisa illata karamin dansu

Kotun Majistare mai lamba 57 da ke Nomanslan ta ci gaba da sauraren shari’ar da ake yi, inda ake zargin wani magidanci da matarsa da laifin hada baki wejen illata wani dansu da bai wuce shekara biyu da haihuwa ba. Mai gabatar da kara, Sajan Usman danladi ya shaida wa kotu cewa tun farko wadanda […]

Ana tuhumar mahaifi da matarsa bisa illata karamin dansu
Ana tuhumar mahaifi da matarsa bisa illata karamin dansu

Kotun Majistare mai lamba 57 da ke Nomanslan ta ci gaba da sauraren shari’ar da ake yi, inda ake zargin wani magidanci da matarsa da laifin hada baki wejen illata wani dansu da bai wuce shekara biyu da haihuwa ba.

Mai gabatar da kara, Sajan Usman danladi ya shaida wa kotu cewa tun farko wadanda ake zargin wato Abdulkadir Uba da sabuwar amaryarsa Sadiya Aliyu sun hada baki, inda suka rika azabtar da yaron har ta kai sun illata shi, inda kansa ya kumbura ga kuma idanunsa ya tabu, kafarsa kuma tuni ta gurgunce.

Takardar karar ta bayayna cewa Abdulkadir ya rabu da mahifiyar yaron mai suna Safiya, wanda hakan ya jawo ya yi sabon aure. Bayan amarya Sadiya ta tare ne sai ya je ya kwato yaron daga hannun mahaifiyarsa, inda kuma ya mika lamarin renonsa gare ta.

Sai dai wadanda ake zargin sun musanta laifin, inda suka danaganta lamarin da shafar aljanu.

A zaman kotun na baya, mai shari’a Haulatu Magaji Kankarofi ta aika da wadanda ake zargin gidan kurkuku, inda a wannan karon ta bayar da belinsu a kan kudi Naira dubu 50 da mutane biyu da za su tsaya musu. An dage sauraren shari’ar zuwa 1 ga Fabrairu mai zuwa.

Lauyan kare marasa galihu a ofishin bayar da kariyar shari’a (PDO), Barista A’isha  Isah Yusuf  ita ce ta sa ido a kan wannan zama na kotun, ta kuma shaida wa kotun cewa ofishin nasu zai ci gaba da sa idanu a kan wannan shari’a don ganin an tababtar da adalci. Ta kuma ja hankalin iyaye da sauran al’umma domin su kauce wa dabi’ar azabtar da ’ya’yan riko, la’akari da kalaman da ake cewa da na kowa ne.