Ana tuhumar makiyaya uku kan garkuwa da mutane a Enugu

Rundunar ’Yan sandan Jihar Enugu ta gabatar da wadansu makiyaya uku masu suna Adamu Mohammed da ake wa lakabi da Suleiman dan asalin Jihar Taraba mai kimanin shekara 25 da Musa Ibrahim dan asalin Jihar Katsina mai shekara 28 sai Dauda Alhaji shi kuma dan asalin Jihar Nasarawa da ake zarginsu da hana al’umomin jihohin […]

Ana tuhumar makiyaya uku kan garkuwa da mutane a Enugu

Rundunar ’Yan sandan Jihar Enugu ta gabatar da wadansu makiyaya uku masu suna Adamu Mohammed da ake wa lakabi da Suleiman dan asalin Jihar Taraba mai kimanin shekara 25 da Musa Ibrahim dan asalin Jihar Katsina mai shekara 28 sai Dauda Alhaji shi kuma dan asalin Jihar Nasarawa da ake zarginsu da hana al’umomin jihohin Ebonyi da Enugu sakat wajen kama mutane suna garkuwa da su domin neman kudin fansa.

Dubun wadanda ake zargin ta cika ne lokacin da ’yan sanda suka kai musu samame a maboyarsu da ke Jihar Ebonyi. Su dai wadanda ake zargin da aka gabatar wa manema labarai, kamar yadda Kakakin Rundunar ’Yan sanda Jihar Enugu ya bayyana, ana zargin su ne suka sace wani Rabaran mai suna Cyprian Uguanyi, na cocin Paul da ke kauyen Olo, Ogbosu Umulokpa a Karamar Hukumar Uzo-Uwani.

Haka zalika ana zargin su ne suka sace Shugabar Mata ta Jam’iyyar PDP a Karamar Hukumar Igbo-Etiti da direbanta da danta suka yi awon gaba da su suna neman kudin fansa. Rundunar ta ci gaba da cewa, wadannan Fulani makiyaya su ake zargi da sace wani mai suna Ejike Uguanyi, cikin wannan wata haka kuma ana zargin su suka sace John Okoli da mahaifiyarsa da kannensa biyu a tsakanin Umumba  a Karamar Hukumar Ezeagu a Jihar Enugu da kauyen Ebenebe da ke Jihar Anambra, kamar yadda rundunar ta sanar.

Rundunar ta ce ta kama wadanda ake zargin da miyagun makamai da suka hada da bindiga kirar AK-47 da harsasai masu yawa. Bayan da aka gama nuna wa manema labarai wadanda ake zargin, Kwamsihinan ’Yan sandan Jihar, Ahmed Abdurrahman, ya ce, “Jami’an rundunarmu ne suka yi ta bibiyarsu a hankali har suka gano maboyarsu a Jihar Ebonyi bayan da suka yi nasarar samun lambar wayar daya daga dakin masu garkuwa da mutanen ta haka suka cimma nasara gano su suka kama su.”

Kwamishinan, ya ce da zarar an gama bincikensu za a mika su ga kotu don ta yanke hukunci a kansu.