Ana tuhumar masu gadi kan fasa shagon gwal a kasuwar Suleja
’Yan sanda a Jihar Neja suna gudanar da bincike a kan wadansu masu gadi biyar da ke aiki a Kasuwar Babangida da ke garin Suleja kan zargin sakaci da aiki bayan fasa wani shagon gwal da ke cikin kasuwar inda aka sace gwala-gwalai da kudin da aka kiyasta sun haura Naira miliyan 10. Lamarin wanda […]

’Yan sanda a Jihar Neja suna gudanar da bincike a kan wadansu masu gadi biyar da ke aiki a Kasuwar Babangida da ke garin Suleja kan zargin sakaci da aiki bayan fasa wani shagon gwal da ke cikin kasuwar inda aka sace gwala-gwalai da kudin da aka kiyasta sun haura Naira miliyan 10.
Lamarin wanda ya faru a ranar Larabar makon jiya da dare, ya jawo zanga-zanga daga wadansu daga cikin ’yan kasuwar tare da rufe shagunansu washegari Alhamis don nuna bacin ransu a kan lamarin.
A zantawarsa da Aminiya mai shagon, Malam Muhammadu Bawa ya ce shi da yaransa sun rufe shagon da misalin karfe shida saura na yammacin ranar, sannan washegari Alhamis bayan yaronsa daya ya zo shagon da misalin karfe 9:00 na safe sai ya samu a balle makulan shagon shida kuma babu ko guda daga cikin jami’an tsaron kasuwar a wurin. “Ya sanar da ni lamarin nan take inda na umarce shi da kada ya bude shagon sai ya sanar da jami’an tsaron kasuwar, inda suka dawo wajen tare kafin aka bude shagon,” inji shi.
Ya ce an sace daukacin kayan da ke cikin shagon da suka hada da tsofaffin gwal da suke saye don sayar wa kamfani da sababbin gwala-gwalai na zamani da kuma azurfa.
Malam Muhammadu Bawa wanda ya ce yana kuma gudanar da harkar canjin kudi a shagon, ya ce an sace masa kudaden Yuro da Dala da Fam da kuma Sefa da kuma nairori. Ya ce akwai kuma wasu kaya da wani makwabcinsa ke ajiya a shagon da su ma aka kwashe, inda jimillar asarar ta kama Naira miliyan 10 da dubu 496 bisa kiyasi, inji shi.
Ya ce akwai nau’u’o’in masu gadi uku da suka hada da ’yan sanda da ’yan banga sai kuma masu gadin kamfani da kungiyarsu ta ’yan kasuwa ta dauka, inda take karbar Naira 600 daga wajen kowane mai shago da ke kasuwar, maishaguna sama da dubu, don samar da tsaro. “Sai dai ni ban zargin kowa ba in ban da masu gadin kamfani da kungiyarmu ta dauka saboda su ne ke yin aikin gadi kai-tsaye tare da yin zirga-zirga a cikin kasuwar da dare.
“Su ’yan sanda zaune suke a waje guda cikin ofishinsu idan ba masu gadin sun nemi daukinsu ba, sannan ’yan banga ba sa ma aiki da dare,” inji shi.
Da yake maida jawabi Shugaban kungiyar ’Yan Kasuwar Suleja, Alhaji Isa Akoshi ya ce yarjejeniyar kungiyarsu da kamafanin gadin shi ne samar da masu gadi 12 a cikin kasuwar dare da rana. Ya ce yana kyautata zaton cewa kamfanin gadin sun mika mutum biyar ne kawai ga ofishin ’yan sanda a lokacin da aka bukace su da hakan a matsayin wani tsari nasu kasancewar ba za su mika daukacin wadanda suka yi gadi a kasuwar ba a lokaci guda.
Babban Jami’in ’Yan sanda na ’A’ Dibision a Suleja, CSP Muhammed A. Muhammed wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya zargi kamfanin gadin da sakaci da aiki ta hanyar gaza zuba wadatattun ma’aikata, Ya ce za su gurfanar da wadanda ake tuhumar a gaban kotu da zarar sun kammala bincike.