Ana tuhumar matasa 40 da shirya taron badala a Bauchi

Jami’an tsaro a Jihar Bauchi sun kama matasa sama da 40 da ake zargi cewa ’ya’yan kungiyar masu luwadi da madigo da suke yin taro a Sakatariyar Gwamnatin Tarayya da ke Bauchi, zargin da wadanda aka kama suka musanta, inda suka ce suna bikin kewayowar ranar haihuwar daya daga cikinsu ne. Kwamishinan Kula da Harkokin […]

Ana tuhumar matasa 40 da shirya taron badala a Bauchi
Ana tuhumar matasa 40 da shirya taron badala a Bauchi

Jami’an tsaro a Jihar Bauchi sun kama matasa sama da 40 da ake zargi cewa ’ya’yan kungiyar masu luwadi da madigo da suke yin taro a Sakatariyar Gwamnatin Tarayya da ke Bauchi, zargin da wadanda aka kama suka musanta, inda suka ce suna bikin kewayowar ranar haihuwar daya daga cikinsu ne.

Kwamishinan Kula da Harkokin Addini na Jihar , Alhaji Ado Aska Zigau ya shaida wa Aminiya cewa “Matasan maza da mata an kama su ne skamakon bayanan asiri da muka samu cewa ’yan kungiyar madigo da luwadi sun yada zango za su yi taro a Bauchi, a babban dakin taro na Sakatariyar Gwamnatin Tarayya. Kan haka ne dukan hukumomin tsaro da suka hada da ’yan sanda da sauransu suka taru muka yi musu kofar rago aka kama su. Suna kan bincike kuma abin da bincke ya tabbatar shi ne matakin da za mu dauka a gaba.”

Kakakin Hukumar ’Yan sandan Jihar Bauchi, DSP Kamal Datti Abubakar ya ce ’yan sanda sun kama mutum 37 amma bayan da suka bincike su sai suka ga ba za su iya tuhumarsu da aikata luwadi ko madigo ba saboda ba wanda aka samu yana aikata haka daga cikinsu. Don haka yanzu sun tura su zuwa kotu suna tuhumar su da aikata taron da bai dace ba.

Da yake zantawa da manema labarai, daya daga cikin wadanda ake zargi, wani matashi dan shekara 18, mai suna Abubakar Adamu ya ce shi ne ya shirya bikin murna kewayowar ranar haihuwarsa, ya kuma gayyaci ’yan uwa da abokan arziki wadanda suka zo taya shi murna amma su ba ’yan luwadi ba ne ba kuma ’yan madigo a cikinsu, illa dai kawai bikin nasu ya zo da tsautsayi.

Ya ce sun ma riga sun kammala bikin suna shirin watsewa ne sai suka ga jami’an tsaro sun zo sun yi musu kofar rago, sun rufe kofar shiga Sakatariyar Gwamnatin Tarayya kuma suka kama su. Ya ce ya yi da-na-sanin shirya irin wannan biki.