Ana tuhumar matashi da yi wa matar dan ci-rani ciki a Jigawa
An gurfanar da wani matashi mai suna Ahmed Muhammed mai shekara 25 a gaban Kotun Lardi ta Shari’ar Musulunci da ke Dutse bisa zarginsa da yi wa matar wani da ya tafi ci-rani a Legas ciki. Lokacin da Alkali Kotun Mai shari’a Muhammed Mustapha ya waiwayi wanda ake tuhumar wato Ahmed Muhammed ya ce gaskiya […]
An gurfanar da wani matashi mai suna Ahmed Muhammed mai shekara 25 a gaban Kotun Lardi ta Shari’ar Musulunci da ke Dutse bisa zarginsa da yi wa matar wani da ya tafi ci-rani a Legas ciki.
Lokacin da Alkali Kotun Mai shari’a Muhammed Mustapha ya waiwayi wanda ake tuhumar wato Ahmed Muhammed ya ce gaskiya ne ya aikata laifin da ake tuhumarsa da shi amma a cewarsa bai san matar aure ba ce sai da ciki ya bayyana daga baya ya rika jin cewa tana da aure. Ya kuma gamsu da bayanan binciken da likitoci suka bayar na cewa cikin nasa ne.
Matar wadda aka sakaya sunanta ta ce matashi ne ya yi mata cikin inda ya rika daukarta suna zuwa wani wuri a garin Kudai yana lalata da ita babu adadi.
Mijin matar Malam Kabiru ya bada shaida cewa ba ya nan ya tafi ci-rani na tsawon wata takwas a Legas inda ya dawo gida ya tarar da matarsa da cikin wata biyar. Ya ce da ya binciki matarsa ne sai ya samu labarin ga wanda ya yi mata cikin alhalin ya bar ta babu ciki, lamarin da ya sa ya sanar da jami’an Hisba wadanda suka gurfanar da su a kotu domin bin neman hakkinsa a wajen wanda ya yi wa masa kwartanci har ciki ya shiga. Alkali Muhammed Mustapha ya dage sauraren karar zuwa mako biyu, kuma ya bayar da belin wanda ake tuhuma kafin kotu ta kammala bincike.
Hukumar Hisba ta karamar Hukumar Dutse ce ta kama Ahmed Muhammed wanda ya fito daga kauyen Kwayamawa a karamar Hukumar Dutse kamar yadda shugaban hukumar Malam Aliyu Galamawa ya sanar da wakilinmu.
Ya ce an kama Ahmed Muhammed ne kan zargin yi wa wata matar aure da mijinta ya tafi ci-rani a Legas ciki, inda ya ce bayan dawowar mijin ne ya matsa wa matar tasa wadda ’yar asalin kauyen Jaudi ne kan ta shaida masa wanda ya yi mata cikin, shi ne ta ce Ahmed Muhammed Kwayamawa ne.
A wata sabuwa Hukumar Hisbar ta kama wani malami da ke koyarwa a makarantar sakandare ta Madobi a karamar Hukumar Dutse bisa zargin yin lalata da ’yar makarantar firamare da ke aji uku a garin na Madobi.
Yarinyar wadda aka sakaya sunanta, iyayenta ne suke aikenta wajen malamin tana kai masa abinci saboda yana koya mata darasi na musamman a gidansu, amma sai malamin mai suna Musa Abdullahi Hadeja ya yaudari yarinyar ya shigar da ita wani kango a kan hanyarta ta zuwa makarantar Islamiyya ya yi lalata da ita.
Yarinyar ta ce malamin ya jima yana lalata da ita a duk lokacin da iyayenta suka tura ta zuwa makaranta ko suka aike ta kai masa abinci, amma bai taba yi mata da karfi ba sai a wannan karo shi ne da ta ji zafi ta yi ihu jama’a suka ji suka kama shi suka gabatar da shi a gaban Hukumar Hisba.