Ana tuhumar shugaban ’yan banga kan mutuwar tsararre a hannunsu
Wani shugaban kungiyar ’yan sintiri da ke kula da yankin Daudu Gyara a garin Suleja ta Jihar Neja, na fuskantar shari’a tare da wani abokin aikinsa da kuma wanda ya kai musu kara a ofishinsu, sakamakon zargin azabtar da wani da suka tsare har ya mutu lokacin da suke tsare da shi a ofishinsu. Marigayin […]
Wani shugaban kungiyar ’yan sintiri da ke kula da yankin Daudu Gyara a garin Suleja ta Jihar Neja, na fuskantar shari’a tare da wani abokin aikinsa da kuma wanda ya kai musu kara a ofishinsu, sakamakon zargin azabtar da wani da suka tsare har ya mutu lokacin da suke tsare da shi a ofishinsu.
Marigayin mai suna Ndubusi Asomughu da ke aikin koyon kafa na’uran satilayit na tsawon shekara guda, mai gidansa mai suna Peter Ageh ne ya kai kararsa a wajen yan bangan, bayan batar wasu kayayyaki a shagonsu, kamar yadda ’yan sanda suka tabbatar wa Aminiya.
Kwamandan yanki na ’yan sandan Suleja, ACP Abubakar Yahaya wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya shaida wa wakilinmu cewa, bayan kama wadanda ake zargi da suka hada da shugaban ’yan bangar, Lawwali Abdullahi da abokin aikinsa Sani Zango da mai gidan marigayin mai suna Peter Ageh, an mika su ga sashin binciken manyan laifuffuka (CID) na rundunar ’yan sandan Jihar Neja da ke Minna, kuma daga can ne za a gurfanar da su a gaban kotu bayan aiwatar da cikakken bincike.
Mahaifin marigayin Mista Clement Asomughu ya ce shugaban ’yan bangan ya kama dansa ne bayan ya yi masa waya da sunan zai ba shi aiki a lokacin da yake cin abincin dare a gidansu. Ya ce bayan daya daga cikin abokan dansa ya garzayo gidansa ya sanar da shi abin da ke faruwa, ya garzaya ofishin ’yan bangan da misalin karfe 9:30 tna dare.
“Na samu dana kwance a kasa cikin mummunan yanayi yana numfashi da kyar yana cewa ruwa, ruwa, na bukaci da a ba ni belinsa don kai shi asibiti, amma sai jagoran ’yan bangar ya ki. Nan na zauna na yi ta kuka tare da mahaifiyar yaron har zuwa karfe 11:30 lokacin da muka yanke shawarar dawowa gida. Da gari ya waye ne na samu labarin cewa danna ya cika a asibiti bayan ’yan bangar sun kai shi sakamakon tabarbarewar lafiyarsa.”
Yanzu haka dai gawar marigayin na ajiye a dakin ajiyar gawa na Asibitin Suleja, kuma mahaifin ya ce bai samu damar ganinta ba.