Ana tuhumar Trump da bai wa ’yar fina-finan batsa toshiyar-baki

Michael Cohen ya ce Trump ya ba da umarnin biyan kudin toshiyar bakin ga Daniels da kuma mace ta biyu.

Ana tuhumar Trump da bai wa ’yar fina-finan batsa toshiyar-baki

Shugaban Amurka, Donald Trump

Masu taimaka wa alkali yanke hukunci na Manhattan da ke birnin New York sun tuhumi Donald Trump kan kudin toshiyar baki da aka biya Stormy Daniels, wata fitacciyar mai fina-finan batsa.

Trump ya zama tsohon shugaba Amurka na farko da ya fuskanci tuhume-tuhume a yayin da yake yin takara ta shiga fadar White House, kamar yadda wata majiyar jami’an tsaro ta fada a ranar Alhamis.

Zarge-zargen, da suka taso daga wani bincike karkashin jagorancin lauyan gundumar Manhattan na jam’iyyar Democrat, Alvin Bragg, suna iya sake fasalin takarar shugaban kasa a 2024.

A baya dai Trump ya ce zai ci gaba da yakin neman zaben fitar da gwani na jam’iyyar Republican, idan aka tuhume shi da wani laifi.

Za a tuhumi tsohon shugaban kasar ne a New York a bisa zargin bayar da wasu makudan kudade na toshiyar-baki, kafin zaben shugaban kasar na 2016, ga Daniel domin hana ta magana kan zargin da ake masa na yin mu’amula da ita.

Bayan rade-radi da aka shafe wata da watanni ana ta yi, yanzu dai ta tabbata za a tuhumi Donald Trump da aikata laifin.

Duk da cewa zuwa yanzu ba a fito fili an bayar da cikakken bayani game da tuhumar ba, amma dai tuhuma ce da ke da alaka da irin rawar da ya taka wajen biyan kudi ga matar – Stormy Daniels.

Kasancewar a yanzu tuhuma ta tabbata a kansa dole ne tsohon shugaban Amurkar ya je New York inda za a dauki hoton zanen yatsunsa da na fuska da kuma na kwayoyin halittarsa.

Daga nan zai gurfana a gaban alkali a kan tuhumar, inda daga nan kuma kila a bayar da belinsa.

Jaridar New York Times ta rawaito cewa, har yanzu dai ba a san takamanman tuhume-tuhumen ba, kuma da alama za a sanar da tuhumar a cikin kwanaki masu zuwa.

Nan take dai ofishin Bragg da lauyan da ke wakiltar Trump ba su amsa bukata ta yin magana ba.

Masu taimaka wa alkali yanke hukuci da Bragg ya gayyato a watan Janairu sun fara sauraron shaidu game da rawar da Trump ya taka wajen biyan Daniels kwanaki kafin zaben shugaban kasa na 2016, wanda ya yi nasara.

Daniels, wacce sananniyar jaruma ce a fina-finan batsa kuma darekta, wacce sunanta na gaskiya Stephanie Clifford, ta ce ta karbi kudin ne a madadin ta yi shiru game da saduwa da ta yi da Trump a shekarar 2006.

Tsohon lauyan Trump, Michael Cohen, ya ce Trump ya ba da umarnin biyan kudin toshiyar bakin ga Daniels da kuma mace ta biyu, tsohuwar mai fitowa a fina finan batsa, Karen McDougal, wacce ita ma ta ce ta yi mu’amalar saduwa da Trump.

Sai dai Trump ya sha musanta cewa yana da alaka da wadannan mata.

Trump ya mayar da martani 

A wata doguwar sanarwa da ya fitar ta mayar da martani kan batun, Mista Trump ya bayyana lamarin da cewa bi-ta-da-kullin siyasa ne kawai ake yi masa.

Kuma lauyoyinsa sun ce ba wani laifi da ya aikata, tare da lasar takobin yakar lamarin a kotu iya karfinsu.

Shi kuwa lauyan matar da ke tsakar wannan zargi, Stormy Daniel, ya ce hukuncin da aka yanke na shari’a kan lamarin ba abin murna ba ne, kuma ba wanda ya fi karfin doka.

Wannan shari’a ka iya kasancewa ta farko a kan tsohon shugaban kasar, inda za a tuhume shi da aikata wani babban laifi.

Amma kuma ba lalle tuhumar ta kasance ta karshe a kansa ba, abu ne da zai zama kamar an bude babi ko sa dan ba kan hakan.

Domin a yanzu haka akwai wasu manyan bincike-bincike da ake yi masa guda biyu, da suka danganci bore da kutsen da aka yi a ginin majalisun dokokin Amurkar, Capitol.

Da kuma yunkurin sauya sakamakon zaben shugaban kasar na 2020, kuma wadannan batutuwa har ma sun fi wannan na yanzu karfi sosai.

A makon da ya gabata Mista Trump ya yi barazanar cewa za a ga balbalin bala’i muddin aka tuhume shi da aikata mugun laifi.

Wanda a kan haka, tsohon mukaddashin shugaban ma’aikata a fadar gwamnatin Amurkar a lokacin Trump, Mick Mulvaney, ya gaya wa BBC cewa, idan har tsohon shugaban kasar ya nemi angiza magoya bayansa su tayar da zaune tsaye a kan tuhumar, to kuwa lalle ya debo ruwan dafa kansa.

Amma kuma ya ce, tuhumar za ta iya taimaka wa Trump, domin ‘yan Republican hatta wadanda ba sa kaunarsa, kamar shi kansa za su tausaya masa da cewa ana yi masa makarkashiya ne ta siyasa ta hanyar amfani da hukumomin gwamnati.

A yakin neman zabe na 2024, Trump ya kere abokanan hamayyarsa na farko don zaben fitar da gwani na jam’iyyarsa, inda a kuri’ar jin rayoyi da Reuters/Iposs suka yi ya nuna yana da goyon bayan kashi 43 cikin 100 na ‘yan Republican, idan aka kwatanta da goyon bayan kashi 31 cikin 100 da abokin hamayyar na kusa, Gwamnan jihar Florida, Ron DeSantis, wanda har yanzu bai sanar da takararsa ba.

Ana dai sa ran Shugaba Biden zai sake neman tsayawa takara.

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50