Ana tuhumar tsohon Sufeta Janar da yin damfara

Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ICPC, a yau Laraba tana tuhumar tsohon sufeta Janar na ‘yan sandan Najeriya Sunday Ehindero da kuma tsohon kwamishinan ‘yan sanda, John Obaniyi akan tuhumarsu da damfarar Naira miliyan 16.4. Babbar kotun tarayya da ke unguwar Apo a Abuja na tuhumar su ne da laifuka […]

Ana tuhumar tsohon Sufeta Janar da yin damfara

Wadume: Kotu da dage sauraron shari’ar kisa

Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ICPC, a yau Laraba tana tuhumar tsohon sufeta Janar na ‘yan sandan Najeriya Sunday Ehindero da kuma tsohon kwamishinan ‘yan sanda, John Obaniyi akan tuhumarsu da damfarar Naira miliyan 16.4.

Babbar kotun tarayya da ke unguwar Apo a Abuja na tuhumar su ne da laifuka 10, ciki harda da aikata damfara da fitar da jawaban karya.

Sai dai tsohon Sufetan bai amince da tuhumar da kotun ke yi masa ba.