Ana tuhumar uwa da hada kai da su kashe mijinta
Rundunar ’Yan sandan Birnin Tarayya, Abuja na ci gaba da bincike a kan wata budurwa ’yar shekara 16 mai suna Imani Kure kan zargin hada kai da mahaifiyarta wajen kashe mahaifinta a kauyen Karaba da ke kusa da garin Bwari, Abuja. Lamarin wanda ya faru a ranar Asabar din makon jiya da tsakar dare, Aminiya […]

Rundunar ’Yan sandan Birnin Tarayya, Abuja na ci gaba da bincike a kan wata budurwa ’yar shekara 16 mai suna Imani Kure kan zargin hada kai da mahaifiyarta wajen kashe mahaifinta a kauyen Karaba da ke kusa da garin Bwari, Abuja.
Lamarin wanda ya faru a ranar Asabar din makon jiya da tsakar dare, Aminiya ta samu labarin cewa yarinyar wadda ’yar kabilar Gbagyi ce ta hada kai da mahaifiyarta ce mai suna Asabe Kure, suka kashe shi, saboda ya ki amincewa da saurayin da za ta aura.
Wakilinmu wanda ya ziyarci kauyen a shekaranjiya Laraba ya tarar da gidan ba kowa, sai dai wadansu mazauna wurin sun bayyana cewa, yarinyar da mahaifiyarta sun yi amfani da adda wajen kashe mijin matar kuma mahaifin budurwar mai suna Mista Kure Isiaka da tsakar dare; lokacin da yake barci bayan ya dawo daga wajen hira a cikin maye.
’Yan sanda sun kama saurayin yarinyar mai suna Nasiru Musa, bayan ya halarci bikin binne gawar Kure tare da kalubalantarsa da ya bayyana idan yarinyar ta shiga, kasancewar ta gudu kuma ba a san inda take ba.
Daga bisani an gano yarinyar a cikin wani daji da ke kusa da kauyen, inda ta bayyana cewa ta aikata laifin ne tare da uwarta, inda ita ma uwar aka kama ta a ranar Litinin.
Babban Jami’in ’Yan sandan Bwari, CSP Biodun Makonjola wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce za a mika mutanen uku ga babban ofishin rundunarsu na Abuja da zarar sun kammala binciken farko.