Ana tuhumar wani matashi da damfarar limamai a Jigawa

Dubun wani matashi mai suna Haruna Abdulrahaman mai kimanin shekara 25 mai damfarar limamai a Jihar Jigawa ta cika a daidai lokacin da ya yi kokarin damfarar wasu manyan mutane. Ana zargin matashin da damfarar Dagacin Sakwaya da ke Masarautar Dutse, Alhaji Suleiman Abdullahi inda ya ce masa shi ne dan Majalisar Mazabar Takai a […]

Ana tuhumar wani matashi da damfarar limamai a Jigawa
Ana tuhumar wani matashi da damfarar limamai a Jigawa

Dubun wani matashi mai suna Haruna Abdulrahaman mai kimanin shekara 25 mai damfarar limamai a Jihar Jigawa ta cika a daidai lokacin da ya yi kokarin damfarar wasu manyan mutane. Ana zargin matashin da damfarar Dagacin Sakwaya da ke Masarautar Dutse, Alhaji Suleiman Abdullahi inda ya ce masa shi ne dan Majalisar Mazabar Takai a Jihar Kano Alhaji Abdulwahab Durbunde kuma ya karbi Naira dubu 25 daga hannunsa da sunan zai ba shi babur. Kuma a kokarin amsar karin wasu kudi ne asirinsa ya tonu lokacin da Dagacin ya sanar da ’yan sanda aka damke shi. An gurfanar da Haruna Abdulrahaman a gaban Kotun Majistare ta garin Takai a ranar Litinin ta makon jiya inda Mai shari’a Tijjani Sale Minjibir ke shari’a bisa tuhumarsa da zambatar wasu manyan mutane ciki har da Limamin Birnin Kudu wanda aka ce ya damfare shi Naira dubu 150 sai kuma Limamin Gaya da ke Jihar kano da Limamin Tsangaya da ke karamar Hukumar Albasu kowanne Naira dubu 100, inda matashin ya rika amfani da sunan dan majalisar Takai yana damfararsu. Alkalin Kotun Majistaren ya dage sauraron karar zuwa ranar 24 ga Maris domin ’yan sanda damar kammala bincike a kan wanda ake tuhumar.