Ana tuhumar wasu Fulani da yi wa dan uwansu duka a Taura
Wasu Fulani makiyaya sun yi wa wani dan uwansu Bafulatani, Mamman Rabe dukan kawo wuka har ya galabaita, inda suka bar shi kwance a kauyen Kayanga da ke cikin karamat Hukumar Taura, Jihar Jigawa. Ya zuwa rubuta labarin nan, ’yan sanda da ke karamar Hukumar Taura sun kama wadanda ake zargi da aikata laifin. Mahaifin […]

Wasu Fulani makiyaya sun yi wa wani dan uwansu Bafulatani, Mamman Rabe dukan kawo wuka har ya galabaita, inda suka bar shi kwance a kauyen Kayanga da ke cikin karamat Hukumar Taura, Jihar Jigawa.
Ya zuwa rubuta labarin nan, ’yan sanda da ke karamar Hukumar Taura sun kama wadanda ake zargi da aikata laifin.
Mahaifin yaron da aka yi wa dukan, Malam Adamu Ado Rugar Kayanga ya shaida wa Aminiya cewa ’yan sanda sun kama wadanda ake zargi amma an bar shi shi kadai yake dawainiya da yaron zuwa asibiti ba tare da taimakon ’yan sanda ba.
Ya ce asali ma yanzu daya daga cikin wadanda ake zargin, an bar shi yana yawo ba tare da an kama shi ba amma daya yana wajen ’yan sanda. Ya kara da cewa yana neman a yi masa adalci.
Da yake bayyana yadda abin ya faru, mahaifin Rabe ya ce kafin su yi wa dansa duka, kiransa suka yi a waya, suka ce ya zo kwari, inda suke yin kiwon shanu. Shi kuma bai san abin da suke nufi ba. Yana zuwa suka fada shi da duka da sanduna sai da suka kai shi kasa, suka bar shi a kwance cikin jinni, yana shure-shure.
Aminiya ta tuntubi Kakakin ’yan sanda a Jihar Jigawa, SP Audu jinjiri game da lamarin, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, inda suke kan bincike. Ya musanta cewa an saki wadanda ake zargi da laifin. Ya ba da tabbacin cewa da zarar sun kammala bincike za su gurfanar das u gaban shari’a.