Ana tuhumar yaro da jefa jariri cikin rijiya
Kotun Majastare ta Ebute Meta a Legas ta bayar da umarnin tsare wani yaro dan shekara 11 a cibiyar lura da kangararrun yara har zuwa ranar 6 ga watan Maris din nan da za a ci gaba da sauraron tuhumar kisan gilla da ake yi wa wannan yaro. ’Yan sanda sun kama yaron ne kan […]
Kotun Majastare ta Ebute Meta a Legas ta bayar da umarnin tsare wani yaro dan shekara 11 a cibiyar lura da kangararrun yara har zuwa ranar 6 ga watan Maris din nan da za a ci gaba da sauraron tuhumar kisan gilla da ake yi wa wannan yaro.
’Yan sanda sun kama yaron ne kan zargin jefa wani jariri dan shekara daya da haihuwa cikin rijiya, inda jaririn ya mutu a rijiyar. Mai gabatar da kara gaban kotun Sufeto Chinalu Uwadione ya shaida wa kotun cewa, yaron wanda kotu ta ce a sakaya sunansa ya aikata laifin ne a ranar 13 ga watan Fabrairu a gida Mai lamba 6 a kan Titin Afolabi Close, a Ojo da karfe 4 na yamma. Ya ce, dangantakar makwabtaka ce ta sa yaron samun damar daukar jaririn daga cikin gidansu ya fita yawo da shi, inda ya jefar da shi cikin rijiyar.
Bayan sauraron karar, Alkalin Kotun Mai shari’a Adeola Adedayo ya bayar da umarnin a tsare yaro a cibiyar kula da kangararrun yara da ke Oregun a Legas har zuwa ranar 6 ga Maris, da za a ji shawarar da Daraktan Shigar da Kararraki (DPP) zai bayar a kan al’amarin.
A wani labarin, Babbar Kotun Majistare ta Yaba a Legas ta bayar da belin wani matashi mai shekara 18 mai suna Malik Moruf da ake tuhuma da laifin sace wayoyin salula da kwamfutoci masu darajar Naira dubu 936.
Mai gabatar da kara Saje Modupe Olaluwoye ta shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma Malik Moruf ya aikata laifin ne a ranakun 28 ga watan Janairu da 12 ga watan Fabrairu a Unguwar Abule-Oja da ke Yaba a Legas.
Ta ce dukan kayan da aka sace mallakar wadansu dalibai 4 ne da ke karatu a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Yaba da ke Legas.
Mai gabatar da karar ta ci gaba da shaida wa kotun cewa, asirin matashin ya tonu ne a yayin da ’yan sanda suka fara binciken kwakwaf, inda suka yi nasarar kama shi a daidai lokacin da yake kokarin balla kofar wani gida da nufin yin sata.
Alkalin Kotun Mai shari’a Oluwatoyin Oghere ta dage sauraron karar zuwa ranar 3 ga watan Afrilu mai zuwa. Ta bayar da belin wanda ake tuhuma kan Naira dubu 200 tare da mutum biyu masu tsaya masa da za su kasance ’yan uwansa ne kuma ma’aikatan gwamnati da takardar biyan haraji cikin asusun Gwamnatin Jihar Legas na tsawon shekara uku.