Ana tuhumarsa da neman matar abokinsa

An gurfanar da wani magidanci a gaban Kotun Shari’ar Musulunci ta Fagge da ke birnin Kano bisa tuhumarsa  da neman matar abokinsa. Da yake shaida wa kotu da’awarsa, mijin matar mai suna Yahaya Baba ya ce abokinsa  mai suna danlami Muhammad yana kokarin ya kwace masa mata, wacce take zaune a gidansu bayan wani dan […]

Ana tuhumarsa da neman matar abokinsa
Ana tuhumarsa da neman matar abokinsa

An gurfanar da wani magidanci a gaban Kotun Shari’ar Musulunci ta Fagge da ke birnin Kano bisa tuhumarsa  da neman matar abokinsa.

Da yake shaida wa kotu da’awarsa, mijin matar mai suna Yahaya Baba ya ce abokinsa  mai suna danlami Muhammad yana kokarin ya kwace masa mata, wacce take zaune a gidansu bayan wani dan sabani da suka samu. “Kasancewar mun samu sabani da matata, wanda hakan ya jawo ta tafi gidansu.
Sai abokin nawa ya je har gidan su matar tawa ya ce ta nemi saki daga wurina inda ya dauki nauyin kai ta kotu don ta shigar da kara. To bayan sun shigar da karar ne har mun je kotun sai daga karshe aka sulhunta, muka yarda za mu koma da aurenmu. A nan ne matar tawa ta gaya min yadda suka yi da abokin nawa.”
Matar (wacce aka boye sunanta) ta shaida wa Aminiya cewa tun kafin wannan lokaci su samu matsala da mijinta, abokin nasa ya dade yana son ya kulla alakar banza da ita. “Da ma tun ina gidan mijina ya sha yi mini waya yana gaya mini kalaman soyayya, inda ni kuma na ki amince wa bukatarsa.
To bayan mun samu sabani da maigidana sai ya zo gidanmu ya same ni ya nuna min cewa kamata ya yi in yi karar maigidana a kotu don a kashe auren. A nan na yarda har ya je ya kai karar, muka shiga kotu da maigidana, a karshe dai aka sulhunta tsakaninmu.”
Da aka tambayi wanda ake zargin, sai ya musanta laifin da ake zarginsa da shi inda ya ce sharri ne kawai matar abokin nasa ta shirya masa.
Alkalin kotun Mai shari’a Abubakar Mahmud Ayagi ya dage shari’ar zuwa mako biyu tare da bayar da umarnin a tsare wanda ake zargin a kurkuku zuwa ranar.