Ana tuhumarsa da satar giyar kusan Naira miliyan uku
Wani matashi mai kimanin shekara 35 mai suna Joshua Effiong ya gurfana a gaban Babbar Kotun Majistare ta Tinubu da ke Legas bisa zarginsa da satar katan 25 na wata giya mai suna Moet da ta kai Naira miliyan biyu da dubu 900. Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa wanda ake tuhumar […]
Wani matashi mai kimanin shekara 35 mai suna Joshua Effiong ya gurfana a gaban Babbar Kotun Majistare ta Tinubu da ke Legas bisa zarginsa da satar katan 25 na wata giya mai suna Moet da ta kai Naira miliyan biyu da dubu 900.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa wanda ake tuhumar ana zarginsa da sace giyar ce daga wata mai suna Adu Elizabeth da take kasuwanci a Close 4, bictoria Garden City da ke Legas.
An gurfanar da Effiong a gaban kotun ne tare da wata ’yar kasuwa mai shekara 40 mai suna Mojisola Bamgbade da ke gida mai lamba 28 a titin Shipeolu a yankin Somolu, wadda ake zargi da sayen giyar daga wanda ake tuhuma, duk da sanin ta sata ne.
Su biyun suna fuskanta tuhume-tuhume hudu na hadin baki don aikata ta’asa da mallakar dukiya ta hanyar karya da sata da kuma karbar kayan sata. Wadanda ake tuhumar sun musanta zargin da ake yi musu.
Tunda farko dan sanda mai gabatar da kara Sufeto Ignatius Okeke ya shaida wa kotu cewa Effiong da wasu da suka gudu sun aikata laifin ne a ranar 28 ga Afrilu da misalin karfe 9 na safe.
Ya Adu ta kai kuka ofishin ’yan sanda a ranar cewa ta kawo katan 25 na giyar ga Effiong kan Naira miliyan biyu da dubu 925 a matsayin bashi, amma bayan an kawo masa giyar sai ya yi layar zana. Ya ce daga baya ne aka kama shi tare da giyar a yankin Bamgbade.
Sufeto Okeke ya ce laifin ya saba wa sashi na 312 da 326 da 409 na dokokin manyan laifuffuka na Jihar Legas na shekarar 2011.
Alkalin kotun Mista L.A. Owolabi ya bayar da umarnin a tsare Effiong a kurkuku, inda ya ce ya rika karya ka’idar beli a shari’o’i da dama a gaban kotun, don haka ba zai sake bayar da belinsa ba.
Sai dai ya bayar da belin abokiyar tuhumarsa kan Naira dubu 400 tare da masu tsaya mata mutum biyu inda ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar Talata mai zuwa.