Ana tuhumarsa da yi wa yarinya ’yar riko fyade
An gurfanar da wani magidanci mai suna Yunusa Abdullahi a Kotun Majistare mai lamba 10 da ke Nomanslan, Kano bisa zarginsa yi wa yarinyar da yake riko fyade, inda a sakamakon haka ya sanya mata cutar kanjamau. Tun da farko dai an fara gurfanar da Yunusa a gaban kotun ne makon da ya gabata, sai […]

An gurfanar da wani magidanci mai suna Yunusa Abdullahi a Kotun Majistare mai lamba 10 da ke Nomanslan, Kano bisa zarginsa yi wa yarinyar da yake riko fyade, inda a sakamakon haka ya sanya mata cutar kanjamau.
Tun da farko dai an fara gurfanar da Yunusa a gaban kotun ne makon da ya gabata, sai dai mai shari’a ta mayar da batun zuwa ofishin ’yan sanda na Shahuci, sashen da ke kula da harkar fyade domin tsananta bincike.
Bayan kammala binciken ne aka gano cewa wanda ake zargin ya yi wa yarinyar (an sakaya sunanta) fyade, wacce ya dauki nauyin rikonta tun daga lokacin yaye. Sai dai ya musa laifin da ake zarginsa da aikatawa, inda ya ce tsautsayi ne ya kai shi ga aikata hakan, domin yana cikin barci sai ya samu kansa a shimfidar yarinyar.
Ana cikin shari’ar ne kuma aka gano cewa wanda ake zargin yana dauke da cuta mai karya garkuwar jiki, inda kuma ya tabbatar wa kotun gaskiyar lamarin.
Mai shari’a, Maryam Ahmad Sabo ta bayar da umarnin tsare wanda ake zargi a gidan maza, inda ta ce a kai yarinyar asibiti don yin bincike ko wanda ake zargin ya sanya mata cutar da yake fama da ita; inda kuma ta dage shari’ar zuwa ranar 3 ga watan Nuwamba mai gabatowa.