Ana yi wa Karan Johar barazana da kisa
A makon jiya ne sanannen mai shirya fina-finai a Indiya, Karan Johar ya kai rahoto ofishin ’yan sanda na birnin Mumbai yana neman a ba shi kariyar tsaro a kullum, saboda a cewarsa yana ci gaba da samun sakonnin barazana, cewa za a kashe shi.Ko a watan da ya gabata ma, dan fim din ya […]

A makon jiya ne sanannen mai shirya fina-finai a Indiya, Karan Johar ya kai rahoto ofishin ’yan sanda na birnin Mumbai yana neman a ba shi kariyar tsaro a kullum, saboda a cewarsa yana ci gaba da samun sakonnin barazana, cewa za a kashe shi.
Ko a watan da ya gabata ma, dan fim din ya shigar da irin wannan koke ga ’yan sandan na Mubai, inda ya ce ana kiransa da wata bakuwar lamba, ana uzura masa da barazanar kisa. Wannan dalili ne ya sa ’yan sandan suka ajiye jami’ansu a unguwar da dan fim din yake zaune. A yanzu kuma Karan yana bukatar a ba shi jami’an da za su rika ba shi kariya a kullum, saboda karuwar barazanar da ake ta yi masa.
dan fim din, wanda kuma shi ne shugaban kamfanin shirya fina-finai na ‘Dharma Pruductions,’ ya taba shigar da irin wannan koke a 2011, bayan da aka yi wa rayuwarsa barazana amma ’yan sanda suka ziyarci unguwarsu, suka duba amma ba su ba shi wata kariya ta musamman ba.
Ganin cewa ba a dauki matakin da ya gamsar da shi ba, Karan ya kara zuwa ofishin ’yan sanda na Khar, inda ya sanar da su cewa an yi masa barazana da kisa ta hanyar sakon tes, don haka yana bukatar a ba shi kariya.
’Yan sanda sun yi zargin cewa wasu bata-gari ne ke yin irin wadannan barazana amma suna ci gaba da bincike. Sun kara da cewa, ba shi kadai aka yi wa irin wannan barazana ba, domin kuwa hatta furodusa Boney Kapoor shi ma an yi masa haka.
Ya zuwa yanzu dai, ’yan sanda sun hada Karan Johar da jami’in kula da lafiyarsa, mai dauke da bindiga. Haka kuma, ’yan sandan sun tura koken nasa zuwa sashen binciken laifuffuka na Mumbai. Sai dai wata majiyar ta ’yan sanda ta ce, wadanda ke aika masa da wadannan sakonnin barazana, suna amfani ne da kafar intanet, don haka suna fuskantar wahala wajen gano maboyarsu.