Ana yi wa rayuwata barazana – Dan takarar Gwamnan PDP a Zamfara

Ya ce harin da aka kai wa matarsa ranar Alhamis ne ya tabbatar masa da hakan

Ana yi wa rayuwata barazana – Dan takarar Gwamnan PDP a Zamfara

Alhaji Dauda Lawal Dare

Dan takarar Gwamnan Jihar Zamfara a jam’iyyar PDP, Dauda Lawal Dare, ya yi zargin ana yunkurin halaka shi.

Zargin nasa na zuwa ne bayan rundunar yaki da daba ta Jihar ta kai wa ayarin motocin matarsa hari da dare Alhamis.

Da yake zantawa da manema labarai ranar Juma’a a Gusau, babban birnin Jihar, dan takarar ya ce matarsa na kan hanyarta ce ta dawowa daga wajen wani taron jam’iyya a Gusau, lokacin da ya ce jami’an rundunar da aka dauki hayarsu sun tare ta sannan suka kai mata harin.

Dauda ya kuma ce, “Sun harba bindigu a kan tawagar matata, wanda a sakamakon haka, ’yan sanda biyu da wasu fararen hula biyar sun ji raunuka, kuma yanzu haka suna can kwance a Cibiyar Lafiya ta Gwamnatin Tarayya da ke Gusau.

“Wannan harin abin kyama wasu bata-garin da aka dauki hayarsu ne suka aiwatar. Dama suna da tarihin cin zarafin mutane, musamman ma ’yan adawa. Amma hakan ba zai sa mu yi kasa a gwiwa ba.

“Muna kira ga dukkan hukumomin tsaron da alhaki ya rataya a wuyansu da su yi cikakken bincike sannan su yi ta maza wajen taka wa ayyukan wannan rundunar birki, wacce gwamnati ke amfani da ita.

“Muna kuma kira ga mutane da kada su tsorata da yunkurin hana su yin zabe, su fito ranar Asabar domin kada kuri’asu, kamar yadda doka ta ba su dama,” in ni shi.

Sai dai Kwamandan rundunar a Jihar, Bello Bakyasuwa, ya karyata zarge-zargen, inda ya ce ba su da tushe ballantana makama.

Ya ce, “Ba aikinmu ba ne kai wa mutane hari. Aikinmu shi ne mu hana ayyikan daba lokacin yakin neman zabe. Abin da kawai na sani shi ne an sami taho-mu-gama tsakanin jami’aina da ’yan dabar da suka fita da su wajen kamfe ranar Alhamis.

“Muna cikin aikin sintiri ne lokacin da muka hangi wasu motoci dauke da makamai suna nuna su. Suna zuwa inda muke suka fara kai mana hari. Yanzu maganar da nake yi da kai an fasa min motata.

“Ba mu da shiri halaka kowa, aikinmu shi ne hana amfani da ’yan daba wajen tayar da zaune tsaye. Wannan ita ce manufarmu. Ba ruwanmu da ko mutum yana cikin jam’iyyar adawa ko mai mulki,” in ji Kwamandan.

“We are not out to assassinate any one but to stop thugs from taking the advantage of the situation to foment trouble. And we care not whether you are  in opposition or ruling party we will stop you. That is our mandate,” Bakyasuwa said.