Ana yin fyade 15 kullum a Kaduna

Babban Alkalin Jihar Kaduna Mai Sharia Muhammad Lawal Bello ya ce ana yin fyade akalla 15 a kullum a jihar. Mai Shari’a Muhammad Lawal Bello ya ce akasarin wadanda ake yi wa fyaden yara mata da maza ne ’yan watanni uku zuwa shakara 12. “Matsalar fyade karuwa take yi a kasar nan har da jihar […]

Ana yin fyade 15 kullum a Kaduna

Babban Alkalin Jihar Kaduna Mai Sharia Muhammad Lawal Bello ya ce ana yin fyade akalla 15 a kullum a jihar.

Mai Shari’a Muhammad Lawal Bello ya ce akasarin wadanda ake yi wa fyaden yara mata da maza ne ’yan watanni uku zuwa shakara 12.

“Matsalar fyade karuwa take yi a kasar nan har da jihar Kaduna domin muna samun fyade kusan 10 zuwa 15 a kullum. 

“Kuma matsalar karuwa take yi inda wadanda abin ke shafa yara ne daga watanni uku zuwa shekaru 12.

“Yadda ake wa ‎yara fyade abin damuwa ne matuka dole a tashi tsaye wajen magance matsalar kafin ya yi muni matuka,” inji shi.

Ya sanar da hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron da Kungiyar Lauyoyin Najeriya Reshen Jihar Kaduna a ranar Litinin.

A jawabinsa, Shugaban kungiyar a jihar Samson Audu kira ya yi ga gwamnati ta tashi tsaye wajen samar da kayan aiki na zamani domin magance kalubalen da sashen Shari’a ke fuskanta.