Ana yunkurin bata gwamnatin Buhari ne – Aliyu Bariri
Shi ma Shugaban Miyetti Allah reshen jahohin Arewa maso gabas, Alhaji Mai Aliyu Usman Biriri, cewa ya yimutanen da ke kara rura wutar rikicin makiyaya da al’ummar kudancin kasar nan suna yin hakan ne a kokarinsu na yi wa gwamnatin Muhammadu Buhari yarfen siyasa don ya fito daga tsatson Fulani.Shugaban ya bayyana hakan ne a […]
Shi ma Shugaban Miyetti Allah reshen jahohin Arewa maso gabas, Alhaji Mai Aliyu Usman Biriri, cewa ya yimutanen da ke kara rura wutar rikicin makiyaya da al’ummar kudancin kasar nan suna yin hakan ne a kokarinsu na yi wa gwamnatin Muhammadu Buhari yarfen siyasa don ya fito daga tsatson Fulani.
Shugaban ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da Aminiya a garin kan hare-haren da ake danganta su da Fulani makiyaya.
Mai Aliyu ya kara da cewa, abin da masu wannan zargin suka mata shi ne, kafin zuwan wannan gwamnati ta Muhammadu Buhari ana samun irin wadannan hare-haren jifa-jifa wani lokacin tsakanin makiya Fulani da manoma, wani lokacin kuma tsakanin Fulani makiyayan da wasu kabilu ko kuma barayin shanu, wadanada aksari za ka tarar da an fi cutar da makiyayan, domin kuwa haka siddan ake bin su daji da wuraren kiwonsu ana kashe su tare da yin awon gaba da dabbobinsu, amma su makiyaya ba su taba dora alhakin hakan ga gwamnatin tsohon shugaba Jonathan ba.
Don haka sai ya gargadi masu rura wutar wannan rikicin da su kwana da sanin cewa mafi yawan al’ummar Nijeriya sun san ba hakan ba ne lamarin, illa dai sun san da cewa ‘’wasu ne ke shigar burtu hade da mugayen iri cikin ‘ya’yanmu na makiyaya ake amfani da su wajen aikta irin wannan ta’assa ta yawaitar hare-hare da yin garkuwa da mutane don karbar kudin fansa.’’