Ana yunkurin kwace makabartar Hausawa a Ibadan – Sarakunan Hausawa
Sarakunan Hausawa da shugabannin al’umma da na kungiyoyi sun yi taron gaggawa kan yunkurin da ake yi don kwace makabatar da suke binne gawarwakin jama’arsu a birnin Ibadan da kewaye. An gudanar da taron ne a Fadar Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin a ranar Asabar da ta gabata. Sarkin Sasa kuma Sardaunan Yamma, Alhaji Haruna […]
Sarakunan Hausawa da shugabannin al’umma da na kungiyoyi sun yi taron gaggawa kan yunkurin da ake yi don kwace makabatar da suke binne gawarwakin jama’arsu a birnin Ibadan da kewaye.
An gudanar da taron ne a Fadar Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin a ranar Asabar da ta gabata.
Sarkin Sasa kuma Sardaunan Yamma, Alhaji Haruna Maiyasin wanda ya shugabancin taron, ya shaida wa mahalarta taron cewa “Mun kira wannan taron gaggawa ne domin tattaunawa a kan wasu muhimman abubuwa biyu da suka shafi batun kwace mana makabartar da muka saya da dimbin kudi muke binne ’yan uwanmu da suka rigamu gidan gaskiya a nan birnin Ibadan da kewaye. Abu na farko da ba mu tabbatar ba ya nuna cewa wai Gwamnatin Tarayya ce za ta karbi filin makabartar domin gina tashar ajiye kwantainonin aikin gina titin jirgin kasa da ya taso daga Legas zuwa Ibadan wanda ya ratsa kusa da makabartar.”
“Na biyu da muka tabbatar shi ne wani kamfanin safiyo mai suna Messers Adeniyi Taiwo and Co. Estate Surbeyors and Balues da ke hanyar Iwo a Ibadan ya turo wakilansa dauke da takardar da ke bukatar karbar makabartar inda suka mika mana. Wannan al’amari ya firgita al’ummar Hausawa mazauna birnin Ibadan da kewaye, shi ne ya sa muka kira wannan taron gaggawa don jin shawarar kowa tsakani da Allah kan matakin da ya kamata mu dauka don kwatar ’yancinmu. Babu wanda ya isa ya karbi wannan makabarta daga hannunmu kuma ina kyautata zaton babu hannun Gwamnatin Tarayya cikin wannan lamari,” inji Sarkin Sasa.
Sarkin Hausawan Ojo Tudun Sunnah, Alhaji Ali Yaro ya shaida wa taron cewa “Muna kukan targade sai ga karaya domin muna cikin tunanin yadda za mu yi maganin masu tone kabari suna sace gawarwaki suna tsafi da sassan jikinsu don neman abin duniya kamar yadda a kwanan baya aka tone kabari biyar a makabartar, sai ga matsalar kwace makabartar baki daya ta taso.”
Ya yi bayanin yadda wakilai uku na kamfanin suka kawo masa takardar da ya karba kuma ya tafi Fadar Sarkin Sasa tare da mutanen domin jin bayanansu da sanin matakin da za a dauka. “Bayan tafiyar wadannan mutane sai Sarkin Sasa ya bayar da umarnin kiran wannan taro domin mu sanar da jama’a halin da ake ciki ba kamar yadda wadansu mutanenmu suke zargin cewa ni Sarkin Hausawan Ojo na sayar da makabarta ba,” inji shi.
Mahalarta taron sun amincewa cewa, ya kamata su dauki lauyoyi domin kai wannan batu gaban kotu. Kuma a fara yin binciken kwakwaf domin gano gaskiyar masu neman kwace makabarta kafin a dauki matakin zuwa kotu. Sannan sun ce ya kamata a hanzarta sanar da Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo da Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar da manyan mutanen Arewa su san halin da ake ciki.
Da yake yi wa Aminiya bayani kan taron, Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin ya ce “Taron ya amince a nada lauya Surajo Danbaba ya fara tuntubar Ma’aikatar Muhalli ta Jihar Oyo domin gano gaskiyar lamarin. Kuma mun nada kwamitin amintattu da za su bi sawun abin da lauyan ya zo dashi domin daukar mataki na gaba.”
Taron ya yi addu’ar Allah Ya tona asirin Hausawan da suke sayar da mutuncinsu wajen karbar kudi domin goyon bayan masu yunkurin kwace makabartar.
Haka an yi amfani da taron wajen tunatar da sarakuna da masu unguwanni kan batun kudin shekara da kowace unguwa take biya da ake amfani da su wajen biyan albashin masu gadin makabartar da sayen kasa domin gyaran kaburbura da injunan sare ciyayi da sauran kayan aiki.
Binciken da Aminiya ta gudanar ya nuna Gwamnatin Jihar Oyo ce take yunkurin karbe makabarta domin gina tashar ajiye kwantainoni da jiragen kasa za su rika daukowa daga Legas zuwa Ibadan.
Aminiya ta jiyo tabbacin ne daga wata majiya a ofishin Kwamishinan Muhalli na Jihar, wadda ta ce “Gaskiya ce takardu masu dauke da batun karbar makabarta sun iso ofishin Kwamishinan amma ba ni da masaniyar abin da ake ciki a yanzu.”
Bayanin da ke kunshe cikin takardar da wakilan kamfanin safiyo na Messrs Adeniyi Taiwo & Co. (Estate Surbeyors) and Baluers da suka mika wa Sarkin Sasa sun nuna cewa gwamnati za ta biya diyyar dukkan filayen da aka karba domin yin wannan aiki.
Daya daga cikin jami’an kamfanin mai suna Ibrahim Shu’aibu da suka sake ganawa da Sarkin Sasa a shekaranjiya Laraba ya shaida wa Aminiya cewa, aikin da suke yi na safiyo a wannan wuri ya shafi dukkan filayen da suke kusa da ainihin wurin da za a gina wannan tashar ce kuma gwamnati za ta biya diyyar filayen da dukkan itatuwa masu albarka a cikin filayen.
Kan haka Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin ya ce, “Ba mu riga mun dauki wani mataki ba tukuna sai idan mun sake zama da dukkan masu ruwa-da-tsaki na makabartar ne za mu yi cikakken bayanin matsayinmu.”