Ana yunkurin tsige Gwamna Nyako
Majalisar Dokokin Jihar Adamawa ta fara yunkurin tsige Gwamnan Jihar, Admira Murtala Hammayero Nyako da Mataimkinsa Bala Ngilari.A shekaranjiya Laraba ne majalisar ta umarci Akawunta ya aika wa Gwamna Nyako da Mataimakinsa Ngalari da sanarwar yunkurin tsige su.Gwamna Murtala Nyako yana faman takun-saka da ’yan majalisar tun lokacin da ya fice daga Jam’iyyar PDP ya […]

Majalisar Dokokin Jihar Adamawa ta fara yunkurin tsige Gwamnan Jihar, Admira Murtala Hammayero Nyako da Mataimkinsa Bala Ngilari.
A shekaranjiya Laraba ne majalisar ta umarci Akawunta ya aika wa Gwamna Nyako da Mataimakinsa Ngalari da sanarwar yunkurin tsige su.
Gwamna Murtala Nyako yana faman takun-saka da ’yan majalisar tun lokacin da ya fice daga Jam’iyyar PDP ya koma Jam’iyyar APC.
Tun a cikin makon jiya aka rika rade-radin cewa ’yan majalisar na yunkurin tsige Gwamnan daga kan kujerarsa.
Duk da babu bayanan kirki kan zaman majalisar na Larabar, amma yanke shawarar fara shirin tsige Gwamna da Mataimakinsa ya dada fito da irin zaman doya da manja da ke tsakanin bangaren zartarwa da bangaren majalisar jihar.
A makon jiya ne siyasar jihar ta dada zafafa bayan da majalisar ta ba da umarnin a kamo wasu kwamishinoni hudu saboda gaza bayyana a gabanta domin amsa tambayoyi kan lamuran kudin jihar.
A wani zaman majsalisar na Alhamis din makon jiya, Mataimakin Shugaban Majalisar Kwamoti Laori na PDP daga Numan, wanda ya jagoranci zaman majalisar ya umarci Kwamishinan ’Yan sandan Jihar ya kama kwamishinonin da suka gaza bayyana a gaban majalisar ya kawo su gabanta a ranar Litinin da karfe 10 na safe.
Kwamishinonin da abin ya shafa sun hada da na aikin gona, Lucy Ishaku da na lafiya, Lilian Stephen da na kasuwanci, Ahmed Gorko da kuma na kasa da safiyo, Abdulrahman Shu’aibu.
Kwamishinan Kudi, Ibrahim bokna da takwaransa na ayyuka Umaru Atiku da Akanta Janar na Jihar Nasir Mohammed sun riga sun bayyana a gaban majalisar. Yayin da majalisar ta bukaci Sakataren Gwamnatin Jihar Kobis Thimnu ya bayyana a gabanta a ranar Litinin da ta gabata, bayan ta samu sakonsa kan gaza bayyana a gabanta a ranar Alhamis saboda wasu dalilai, lamarin da ya jawo aka rika yada jita-jitar cewa majalisar ta ja dagar ta tsige Gwamnan.
A ranar 27 ga Mayu ne majlisar ta ba Gwamna Nyako da gwamnatinsa wa’adin yini uku ta biya ma’aikatan jihar dukkan kudinsu da ta zabtare daga alawus dinsu na Mayun 2014.