Ana zabe lafiya a Kaduna

Mutanen Jihar Kaduna sun fito domin kada kur’arsu kamar yadda doka ta tanada musu. Wakilinmu da zagaya, ya gane wa idonsa yadda mutane suka fito suka tsaya a kan layi ba tare da rikici. Wani wakilin Jam’iyyar APC a Unguwar Hayin Banki da ke Karamar Hukumar ta Arewa, Injiniya Rabi’u Ibrahim wanda aka fi sani […]

Ana zabe lafiya a Kaduna

Mutanen Jihar Kaduna sun fito domin kada kur’arsu kamar yadda doka ta tanada musu.

Wakilinmu da zagaya, ya gane wa idonsa yadda mutane suka fito suka tsaya a kan layi ba tare da rikici.

Wani wakilin Jam’iyyar APC a Unguwar Hayin Banki da ke Karamar Hukumar ta Arewa, Injiniya Rabi’u Ibrahim wanda aka fi sani da Rabe mai gaya ya bayyana mana cewa zabe yana lafiya daidai.

Hakanan kuma wakilinmu ya rawaito mana cewa an zuba jami’an tsaro sosai domin hana tayar da hankali.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa