Ana zaman ɗarɗar bayan an wayi gari da sarakuna biyu a Kano

Ganduje da Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro na neman dawo da Sarki kujerarsa.

Ana zaman ɗarɗar bayan an wayi gari da sarakuna biyu a Kano

An shiga rudani bayan wayar gari da sarakuna biyu a Jihar Kano, inda Sarki Muhammadu Sanusi II yake zaune a Fadar Sarki da ake kira Gidan Rumfa, yayin da Sarki Aminu Bayero ya ke nasa zaman fadar a Fadar Sarki da ke Nassarawa.

A halin yanzu dai jami’an tsaro sun yi wa duk fadojin biyu kawanya, inda sarakunan biyu ke zaune a ciki.

Aminiya ta samu rahoton cewa, cikin dare duk sarakunan biyu suka shiga fadojin, inda bayanai ke cewa Sarki Sanusi II ya shiga Gidan Rumfa da misalin karfe 3:00 na dare tare da rakiyar Mataimakin Gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam.

Haka kuma, wasu sojoji sun mamaye Fadar Sarkin Kano da ke unguwar Nassarawa inda Sarki Aminu Ado Bayero wanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tubewa rawani a ranar Alhamis ya yada zango.

Ana iya tuna cewa, a yayin da yake rattaba hannu kan sabuwar dokar ta rushe masarautun jihar biyar, Gwamnan ya bai wa Sarakunan da ake tubewa rawani umanin tattara ina-su-ina-su cikin awa 48.

A yayin da duk sauran sarakunan — da suka hada da Alhaji Nasiru Ado Bayero na Bichi, da Alhaji Kabiru Muhammad na Rano, da Alhaji Ibrahim Abubakar II na Karaye da kuma Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir na Gaya —  sun cika umarnin gwamnan, sai ga shi Aminu Ado Bayero ya shigo cikin Birnin Dabo da safiyar wannan Asabar.

Bayanai sun ce jirgin da ya yi jigilar Sarki Aminu ya dira a Filin Jirgin Saman Malam Amiu Kano da misalin kare 4.30 na safiya, inda magoya baya suka rika fitowa tarbarsa suna rera wasu ayoyi na Suratul Fatiha.

A nan dai Sarki Aminu ya yi sallar Asuba sannan ya garzaya Fadar Sarki da ke Nassarawa.

Wannan lamari ya sanya aka shiga zaman dardar a Kano a yayin da ake zargin jami’an tsaro suna kokarin shigar da Sarki Aminu Ado Bayero Babbar Fada da ke Kofar Kudu.

Sai dai da yake martani kan lamarin, Gwamna Abba Kabir ya bayar da umarnin kama Sarkin Aminu Ado Bayero yana mai zarginsa da kokarin tayar da zaune tsaye a jihar.

Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanya wa hannu ta ce a matsayinsa gwamnan na shugaban tsaron jihar, ya dauki wannan matakin ne don tabbatar da cikakken tsaro a jihar da kewayenta.

A jawabinsa, Mataimakin Gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam, ya bayyana cewa “mun sami labari cewa Dokta Abdullahi Umar Ganduje ne ya je wajen Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro, [Nuhu Ribadu] suke kokarin bankara lamarin wajen ganin sun dawo da tsohon Sarkin Kano kujerarsa”

Kwamared Aminu Abdulsalam ya kuma sha alwashin cewa za su ci gaba da zama a fadar har sai sun ga abubuwa sun daidaita