Ana zaman dar-dar kan dakatar da Hakimi a yankin Gassol
Ana zaman dar-dar a garin Tella da ke karamar Hukumar Gassol a Jihar Taraba sakamakon dakatar da Hakimin yankin Jiddawo wanda wani bangare ne na garin Tella kan wasu dalilai da ake kyautata zaton cewa suna da alaka da siyasa. Hakimin na Jiddawo Alhaji Isa Ciroma an nada shi ne ’yan watannin baya amma a […]
Ana zaman dar-dar a garin Tella da ke karamar Hukumar Gassol a Jihar Taraba sakamakon dakatar da Hakimin yankin Jiddawo wanda wani bangare ne na garin Tella kan wasu dalilai da ake kyautata zaton cewa suna da alaka da siyasa.
Hakimin na Jiddawo Alhaji Isa Ciroma an nada shi ne ’yan watannin baya amma a makon jiya sai aka tura masa wata wasika daga Ma’aikatar kananan Hukumomi da Al’amuran Masarautu cewa an dakatar da shi daga kan mukaminsa.
Takardar dakatarwar wadda ke dauke da sa hannun Babban Sakatare a ma’aikatar, Alhaji Bello Yerro ta umurci Hakimin ya daina gudanar da dukkan ayyukansa na hakimci.
Kamar yadda bayanai suka nuna jama’ar masarautan sun tunzura wanda hakan ya haifar da zanga-zangar kin amincewa da dakatar da Hakimin.
Shi dai Alhaji Isa Ciroma inji wata majiya ana zargin cewa bai taimaka wa Jam’iyyar PDP mai mulki a jihar ba a lokutan zabubbukan da suka gabata wanda haka ya sa ya gamu da fushin gwamnati.
Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa gwamnatin jihar ta tura shugaban kwamitin riko na karamar hukumar Alhaji Tukura Bashiru zuwa masarautar don ba jama’a hakuri kan dakatawar da aka yi wa Hakimin.
Majiyar ta shaida wa wakilinmu cewa yana isa sai matasa suka fara zanga-zanga wadda ta tilasta wa shugaban barin garin cikin gaggawa.
Majiyar ta ce jama’ar masarautar sun ce ba za su amince a nada musu wani sabon Hakimi ba sai dai a maido musu da wanda aka dakatar in ana son zaman lafiya a masarautar.
kokarin da wakilimu ya yi don jin ta bakin Babban Sakataren Ma’aikatar kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu ta Jihar Alhaji Bello Yerro ya ci tura. Amma Shugaban karamar Hukumar Gassol Alhaji Tukura Bashiru ya shaida wa wakilinmu ta waya cewa a ’yan kwanakin baya ne aka samu ’yar hatsaniya kan dakatar da Hakimin na Jiddawo amma yanzu komai ya lafa.