Ana zaman makokin mutuwar kunkuru mai shekaru 344 a fadar Ogbomoso
Yanzu haka fadar Soun na (Sarkin) Ogbomoso a Jihar Oyo tana ci gaba da zaman makokin mutuwar wani kunkuru da ta ce shi ne mafi tsufa a Afrika wanda ya mutu a ranar Alhamis din makon jiya bayan ya shafe shekara 344 a duniya. Kunkuru namiji ana kiransa da Alagba, kuma ya yi rayuwarsa ce […]
Yanzu haka fadar Soun na (Sarkin) Ogbomoso a Jihar Oyo tana ci gaba da zaman makokin mutuwar wani kunkuru da ta ce shi ne mafi tsufa a Afrika wanda ya mutu a ranar Alhamis din makon jiya bayan ya shafe shekara 344 a duniya. Kunkuru namiji ana kiransa da Alagba, kuma ya yi rayuwarsa ce a wani kebabben wuri da ake kiwonsa a cikin fadar Soun na Ogbomoso, Oba Jimoh Oladunni Oyewumi wanda shi yake daukar dawainiyar kunkurun tun daga 1974 da ya hau karaga. Kunkurun ya mutu ne bayan fama da rashin lafiya. Da yake yi wa ’yan jarida karin haske Sakataren Soun na Ogbomoso Mista Ajamu Oluwatoyin ya ce fadar Sarki ta yanke shawarar ba za a binne kunkuru ba, maimakon haka za a adana gawar ce a wani wuri na musamman inda za a gayyaci likitoci su yi amfani da sinadarin hana gawar rubewa domin shiga cikin kundin tarihi.
Kafin mutuwar kunkuru Alagba masu yawon bude ido na ciki da wajen Najeriya ne suke zuwa fadar Soun da ke Ogbomoso domin ganin kunkurun da ke shan ruwa lita 25 sau daya a mako biyu.
Bayanan da Aminiya ta samu sun ce Alagba ba ya cin nau’in abincin da dan Adam yake ci amma yana cin gwanda da wasu nau’o’in tsirrai kuma an kiyasta nauyinsa a kan kilo100 ko wato nauyin buhun siminti biyu. Masu kiwon Alagba sun ce yana son yanayi irin na damina inda yake gudanar da wasu abubuwa na sha’awa da mamaki amma ba ya son yanayi irin na bazara lokacin zafi. Kattin mutum hudu ne suke iya daukar wannan kunkuru zuwa wani wuri ko ajiye shi a cikin mota.
Masu yawon bude ido sukan hau kokon bayan kunkurun ya rika tafiya da su a goye a iyakar wurin da ake kiwonsa. Sun ce komai nauyin mutum kunkuru zai iya goya shi a bayansa ya yi tafiya da shi. Soun na Ogbomoso Oba Jimoh Oladunni Oyewumi ne ya hana hawa kunkurun a dalilin manyantarsa.
An ce Sarki wato Soun na Ogbomoso na uku, Oba Ikumoyede Ajao da aka haife shi a karni na 16 kuma ya yi mulki a karni na 17 ne ya fara kiwon kunkurun a fadarsa.
Mista Muftau Owolabi dan sanda ne kuma odilan Soun na Ogbomoso ya ce Alagba ya fara rashin lafiya ne shekara 3 da suka gabata har aka yi masa fida a wuyansa. Likitoci sun yi kokarin ceto rayuwarsa da kashi 50 na aikin fidar da suka yi.
Akwai mutum biyu masu lura da kunkurun wadanda aka dora musu alhakin abincinsa da kula da lafiyarsa da sauran bukatu da Soun na Ogbomoso yake daukar nauyinsu da kuma kunkurun.