An yi zanga-zanga bayan sake kai hari a Faskari
Al’ummar Karamar Hukumar Faskari na zanga-zanga saboda yadda yankin ya koma tamkar babu tsaro sakamakon yawaitar hare-haren ’yan bindiga. Kwana daya da kai hari a garin Kadisau, sai ga shi a safiyar Alhamis mahara sun sake kai wani harin a garin na Faskari. Rashin Tsaro: Matasa sun yi bore a Katsina ‘Yan bindiga sun kashe […]
Masu zanga-zangar rashin tsaro a garin ‘Yantumaki a Jihar Katsina
Al’ummar Karamar Hukumar Faskari na zanga-zanga saboda yadda yankin ya koma tamkar babu tsaro sakamakon yawaitar hare-haren ’yan bindiga.
Kwana daya da kai hari a garin Kadisau, sai ga shi a safiyar Alhamis mahara sun sake kai wani harin a garin na Faskari.
- Rashin Tsaro: Matasa sun yi bore a Katsina
- ‘Yan bindiga sun kashe Hakimin ‘Yantumaki
- Hotuna: Yadda aka yi da zanga-zangar rashin tsaro a Katsina
Hakan ya sa mutanen garin da ma makwabtansu daga yankin ‘Yankara gudananar da zanga-zangar.
Kwana hudu ke nan da yin irin wannan zanga-zangar a garin ‘Yantumaki ta karamar hukumar Dannusa.