Ana zanga-zangar adawa da gwamnatin Bashar al-Assad a Siriya

Siriyawa na bore kan yadda kasashen Larabawa ke kulla sabuwar dangartaka da Bashar al-Assad.

Ana zanga-zangar adawa da gwamnatin Bashar al-Assad a Siriya

Daruruwan al’ummar kasar Siriya sun gudanar da zanga-zanga don yin Allah wadai da yadda kasashen Larabawa ke kulla wata sabuwar dangantaka da gwamnatin Bashar al-Assad.

Boren da ya gudana a birnin Idlib na zuwa ne mako guda bayan da Ministan Harkokin Kasashen Ketare na Saudiyya ya gana shugaba Bashar al-Assad birnin Damascus.

Bayanai sun ce wannan ziyara ta zama irinta ta farko a shekaru 12 bayan da yaki ya barke a kasar.

Kazalika jami’an diflomasiyyar kasashen Saudiyya da Tunisiya da Masar sun yi wata ganawa da ke da zummar lalubo hanyoyin kawo karshen yakin da ya daidaita kasar.

Siriyawan dai na neman kasashen duniya musamman na yankin Gabas ta Tsakiya da su ci gaba da mayar da shugabansu saniyar ware, saboda ba sa son kowacce kasa ta saka musu baki don ba za su taba daidaitawa da al- Assad ba.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno