Ana zanga-zangar neman kama El-Rufai a Kaduna
Uba Sani ya yi ƙorafi saboda ɗimbin bashin da ya gada a wurin gwamnatin da ta gabata.
Wasu masu zanga-zangar ƙarƙashin inuwar ƙungiyar Kaduna Citizens Watch for Good Governance (KCWGG) sun mamaye gidan gwamnati da ke Kaduna a wannan Alhamis ɗin.
Ana zanga-zangar ce domin neman a binciki tsohon Gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufai tare da kama shi.
Sun buƙaci Gwamna mai ci Uba Sani da ya gayyaci jami’an Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) da sauran hukumomin da abin ya shafa domin su kama El-Rufai tare da gurfanar da shi a gaban ƙuliya bisa zargin gwamnatinsa da karkatar da zunzurutun kudi har Naira biliyan 423.
Masu zanga-zangar sun yi ta rera waƙoƙin suna bayyana buƙatar ɗauke da kwalaye da alluna masu rubuce-rubuce daban-daban.
Wasu daga cikin rubutun na cewa, ‘Za mu mamaye dukkan Ma’aikatu don korar duk waɗanda ake tuhuma a cikin rahoton’. Da kuma “A daina ba da duk lamunin da ba a bi ƙa’ida ba kafin a miƙa shi.”
A ranar 30 ga Maris, 2024, Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa Jihar Kaduna na fuskantar ɗimbin bashin da ya kai dala miliyan 587, da Naira biliyan 85, da kuma bashin kwangila 115 da ya gada daga gwamnatin da ta gabata.