Ana zanga-zangar neman tsige kwamishina a Jigawa

Masu zanga-zangar sun bayyana cewa murabus ɗin Kwamishinan zai zama babbar nasara ga dimokuraɗiyya.

Ana zanga-zangar neman tsige kwamishina a Jigawa

Daruruwan mutane sun gudanar da zanga-zangar neman tsige Kwamishinan Harkokin Noma da Albarkatun Kasa na Jihar Jigawa, Alhaji Muttaka Namadi.

Jama’ar waɗanda suka fito daga mazabar Ringim sun yi zanga-zangar ce a gaban Fadar Gwamnatin Jigawa a ranar Alhamis.

Masu zanga-zangar da suka haɗa manoma, matasa, shugabannin al’umma da kuma mata sun yi tattakin ne daga garin Ringim zuwa gidan Gwamnatin Jigawa riƙe da kwalaye da alluna masu ɗauke da saƙonni daban-daban.

Sun yi ta yekuwar bayyana rashin jin daɗinsa musamman kan abin da suka kira rashin kwazon daga bangaren kwamishinan suna masu kiran da ya yi murabus.

A cewar jagoran masu zanga-zangar, Mallam Bashir Muhammad DanMalam, kwamishinan ya gaza aiwatar da wani aiki da ya dace da muradun al’umma.

“Saboda haka lokaci ya yi da zai yi murabus ko kuma ya ci gaba da fuskantar adawa daga ɓangarenmu,” inji DanMalam.

Masu zanga-zangar waɗanda suka alaƙanta kwamishinan da watsi da nauyin da rataya a wuyansa da kuma rashin ƙwarewar aiki, sun bayyana cewa murabus ɗinsa zai zama babbar nasara ga dimokuraɗiyya.

Aminiya ta ruwaito cewa duk da ƙoƙarin da jami’an tsaro da wasu wakilan gwamnati suka yi wajen rarrashi da shiga tsakani, masu zanga-zangar sun yi biris da cewa lallai sai Gwamna Umar Namadi ya saurari buƙatarsu.

Bayan shafe aƙalla sa’o’i biyu ana zanga-zangar ce, aka zaɓi wasu daga cikinsu a matsayin wakilai domin su miƙa wa gwamnan kokensu a hukumance.

Wannan zanga-zangar dai ta ƙara fito da yadda al’ummar Jigawa ke muradin jagoranci nagari daga ɓangaren jami’an gwamnati.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara