Ana zargin alkalai 34 da karbar na goro a Ghana
A makon jiya ne cikin alkalan kasar Ghana ya duri ruwa lokacin da wani dan jarida ya bayyana cewa ya kwashe shekara biyu yana binciken irin wainar da ake toyawa a kutunan kasar.Ya dai ambaci sunayen alkalai guda 34 da ya ce ya same su da hannu dumu-dumu suna karbar na goro, inda ya ce […]
A makon jiya ne cikin alkalan kasar Ghana ya duri ruwa lokacin da wani dan jarida ya bayyana cewa ya kwashe shekara biyu yana binciken irin wainar da ake toyawa a kutunan kasar.
Ya dai ambaci sunayen alkalai guda 34 da ya ce ya same su da hannu dumu-dumu suna karbar na goro, inda ya ce ya nadi muryoyinsu a lokuta daban-daban da al’amarin ya faru.
dan jaridan mai suna, Anas Armiyawu Anas, shahararre ne wurin binciken kwakwab, inda yake batar da kamanninsa don gano labarai. Yakan gudanar da irin wannan bincike, inda yake tona asirin irin abubuwan asha da ake tafka wa a ma’aikatu da wurare daban-daban.
Kodayake, an fara gasgata ikirarin dan jaridan ne bayan yanda alkalai uku sun sume bayan da jin labarin. Har ila yau, kawo yanzu hukuma ta dakatar da 22 daga aiki.
Abin da ake ci gaba da takaddama a kai a kasar shi ne ko ya halarta a nuna wa jama’a faya-fayan bidiyon da dan jaridar ya nada, wadanda suke nuna lokutan da akalan suke aikata ba daidai ba, ko kuma a’a.