Ana zargin baduku da yi wa ’yar shekara 7 fyade

Yan sanda a garin Karmo, Abuja na binciken wani baduku mai shekara 60 mai suna Habibu Maikada Safana kan zargin yi wa yarinya ’yar shekara 7 fyade. Mutumin wanda baduku ne da ke sana’ar gyaran takalma, bayanai sun ce wani makwabcinsa  a wurin sana’a ne ya ankarar da mahaifiyar yarinyar bayan ya kula da yadda […]

Ana zargin baduku da yi wa ’yar shekara 7 fyade
Ana zargin baduku da yi wa ’yar shekara 7 fyade

Yan sanda a garin Karmo, Abuja na binciken wani baduku mai shekara 60 mai suna Habibu Maikada Safana kan zargin yi wa yarinya ’yar shekara 7 fyade. Mutumin wanda baduku ne da ke sana’ar gyaran takalma, bayanai sun ce wani makwabcinsa  a wurin sana’a ne ya ankarar da mahaifiyar yarinyar bayan ya kula da yadda take zuwa shagon mutumin a lokacin makaranta ko aiki.

Sarkin Hausawan Mpape, Malam Amiru Buhari wanda ya jagoranci gabatar da lamarin a gaban ’yan sanda ya shaida wa Aminiya cewa, daga nan ne kuma sai mahaifiyar yarinyar ta tunkari yarinyar da maganar inda ta tuhume ta a kan matsalar ciwon ciki da take yawan fama da shi. Ya ce yarinyar ta shaida wa mahaifiyarta cewa mutumin na taba mata al’aurarta sannan kuma ya yi mata fyade.

Sarkin Hausawa ya ce,  yan bangar  kauyen ne suka kama mutumin tare da mika shi ga ofishin ’yan sandan inda ya amince da aikata abin da a ke zarginsa da shi.                                                                                          Ya ce kuma yarinyar ta ambaci sunan wani direban tifa da aikata lalata da ita, sai dai ya ce direban wanda dan asalin Jihar Neja ne da ke da daki a kauyen, ya sulale bayan samun labarin zarginsa da aka yi.

Babban jami’in ’yan sanda na Garin Karmo, CSP Alhassan Ahmad wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an kai yarinyar Asibitin Gwarinpa don tantace lafiyarta sannan bayan samun sakamako za su mika mutumin ga sashen binciken manyan laifuffuka na ’yan sandan Abuja, don ci gaba da bincike a kan lamarin.