Ana zargin birkiloli biyu da yi wa ’yan firamare fyade
A ranar asabar da ta gabata ne wadansu iyayen yara mazauna Unguwar Kakaki da ke cikin birnin Zariya suka kai korafi ofishin ‘yan sanda da ke cikin birnin Zariya suna zargin wadansu magidanta da bata musu yara ‘yan makarantar firamare, inda nan da nan ‘yan sanda suka kamo wadanda ake zargin.Wadanda ake zargin sune, Idi […]

A ranar asabar da ta gabata ne wadansu iyayen yara mazauna Unguwar Kakaki da ke cikin birnin Zariya suka kai korafi ofishin ‘yan sanda da ke cikin birnin Zariya suna zargin wadansu magidanta da bata musu yara ‘yan makarantar firamare, inda nan da nan ‘yan sanda suka kamo wadanda ake zargin.
Wadanda ake zargin sune, Idi Haruna mai shekaru 39 da kuma Nuhu Adamu mai shekaru 35, wadanda suke zaune a gida daya a Unguwar Kakaki cikin birnin Zariya, kuma dukkansu suna sana’ar gini ne.
Da wakilimu ya zanta da wadanda ake zargin sun musanta zargin da ake yi musu na lalata da kananan yara. Sai dai daya daga cikinsu mai suna Nuhu Adamu ya ce yaran suna samunsu a wurin da suke aiki ne su rika damunsu da su ba su kudi, ‘ Har ma su rika sanya wa Idi Haruna hannu a aljihu, domin shi mutum ne mai son wasa da kananan yara. A lokacin da suke sanya masa hannu a aljihu, cikin kudin aikinmu da aka ba shi ya ba mu, Naira dubu daya ta bace. Amma cewa da suka yi wai muna lalata da su sam ba haka ba ne.’
Shi kuwa Idi Haruna cewa ya yi, shi yana da mata daya da yara shida, kuma shi asalinsa mutumin Sabon birnin Gobir ne, kuma akalla ya shekara goma sha takwas a birnin Zariya.
Yaran biyu da ake zargin suna lalata da su, daya yarinyar ‘yar shekara goma sha biyar ce, dayar kuma ‘yar shekara goma sha hudu, wadanda dukkansu suna karatu ne a makarantan firamare da ake kira Galadima Adamu Badokaje, kuma sun tabbatar da cewa wadannan mutanen suna lalata da su, a inda suka ce idan sun aikata lalatar suna ba su Naira hamsin ko dari.
Aminiya ta garzaya Unguwar Kakaki, unguwar wadannan da ake zargi da yin lalata yaran domin jin ta bakin mazauna wannan yankin, inda wata majiya ta sheda wa wakilinmu cewa shi Malam Idi an taba korarsa a gidan da yake haya akan al’ amari makamancin wannan, kuma ya tabbatar da cewa lailai biri ya yi kama da mutum, domin irin yadda yake yawan wasa da kananan yara.
Ita kuma rundunar ‘yan sanda da koken ke gabanta, da wakilinmu ya tuntube ta cewa ta yi tana nan tana cigaba da bincike domin gano yadda lamarin yake gudana.