Ana zargin dalibin jami’a da kisan almajiri a Kano
A ranar Litinin da ta gabata ce aka zargi wani dalibin Jami’ar Kimiiyya da Fasaha ta Wudil da kashe wani almajiri mai suna Adamu Ibrahim mai kimanin shekara 18 a Unguwar Sabon Garin ’Yan Kwaya da ke Karamar Hukumar Wudil a Jihar Kano. Aminiya ta gano cewa dalibin wanda aka bayyana sunansa a matsayin Lubsi ya […]
A ranar Litinin da ta gabata ce aka zargi wani dalibin Jami’ar Kimiiyya da Fasaha ta Wudil da kashe wani almajiri mai suna Adamu Ibrahim mai kimanin shekara 18 a Unguwar Sabon Garin ’Yan Kwaya da ke Karamar Hukumar Wudil a Jihar Kano.
Aminiya ta gano cewa dalibin wanda aka bayyana sunansa a matsayin Lubsi ya yi wannan aika-aikar ce a lokacin da ya je diban ruwa a wata rijiya da ke kusa da jami’ar
Wani wanda lamarin ya faru a kan idonsa mai suna Husaini Ibrahim ya ce shi da marigayin suna tare suna diban ruwa lokacin da wanda ake zargin ya zo ya nemi dole sai sun ba shi dama ya fara dibar ruwan.
Da suka nuna kin amincewarsu ne wanda ake zargin ya dauki katako ya buga wa marigayin inda a take ya fadi kasa lamarin da ya sa aka garzaya da shi asibiti inda rai ya yi halinsa.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano DSP Abdullahi Haruna ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai a lokacin wanda ake zargi ya gudu kuma ’yan sanda na gudanar da bincike don ganin ya shiga hannunsu.
Sai dai wata sanarwa ta ce hukumomin jami’ar sun mika dalibin ga ’yan sanda a shekaraniya Laraba kamar yadda Kakakin Jami’ar Sa’idu Na’iya ya fadi a wata sanarwa.