Ana zargin dan kasuwa da zambar Naira miliyan daya da rabi
Kotun Majistare mai lamba 10 da ke Nomanslan a Jihar Kano ta gurfanar da wani magidanci gabanta bisa zarginsa da yin zamba cikin aminci, inda ya cuci wata mata kudi har kimanin Naira miliyan daya da rabi. Mai gabatar da kara, ASP Shehu Musa ya shaida wa kotu cewa wata mata ce mai suna Aisha […]
Kotun Majistare mai lamba 10 da ke Nomanslan a Jihar Kano ta gurfanar da wani magidanci gabanta bisa zarginsa da yin zamba cikin aminci, inda ya cuci wata mata kudi har kimanin Naira miliyan daya da rabi.
Mai gabatar da kara, ASP Shehu Musa ya shaida wa kotu cewa wata mata ce mai suna Aisha Ibrahim Yakasai ta yi karar wani abokin kasuwancinta mai suna Isa Jauro, inda ta ce shekaru hudu da suka wuce lokacin tana kasar Saudiyya ta amince wa Isa Jauro, har ta ba shi wasu kaya da kimarsu ta kai Naira miliyan daya da rabi da niyyar ya kai mata su Najeriya.
Mai gabatar da karar ya ci gaba da cewa “amma maimakon ka auna mata kayan zuwa gida Najeriya sai ka karkatar da su inda suka zama mallakarka”
Sai dai wanda ake kara ya musanta laifukan da ake zargin nasa da su da suka hada da cin amana da cuta da wulakanta dukiya, laifukan da mai gabatar karar ya ce sun saba wa sashe na 313 da 320 da 306 na Kundin Shari’ar Pinal Kod.
Alkalin kotun, Mai shari’a Maryam Ahmed Sabo ta amince da bayar da belin wanda ake zargi bayan lauyansa ya yi roko a kan hakan. Haka kuma ta dage sauraren shari’ar zuwa ranar 20 ga watan Nuwambar nan da muke ciki.