Ana zargin dan majalisa da cinye kudin ubangidansa

A ci gaba da sauraren karar da wani dattijo, Alhaji Aminu Muhamamd ya yi na dan Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar karamar Hukumar Nasarawa, Alhaji Ahmad Ibrahim Gama, wanda aka fi sani da Lugard a gaban kotun majistare ta Gyadi-Gyadi kan zargin hadin baki da ya yi da wasu mutane inda suka yi awon […]

Ana zargin dan majalisa da cinye kudin ubangidansa
Ana zargin dan majalisa da cinye kudin ubangidansa

A ci gaba da sauraren karar da wani dattijo, Alhaji Aminu Muhamamd ya yi na dan Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar karamar Hukumar Nasarawa, Alhaji Ahmad Ibrahim Gama, wanda aka fi sani da Lugard a gaban kotun majistare ta Gyadi-Gyadi kan zargin hadin baki da ya yi da wasu mutane inda suka yi awon gaba da makudan kudinsa.
Tunda farko mai gabatar da kara Bala Ahmad ya ce Alhaji Aminu ya yi karar dan majalisar ne saboda yi masa sama da fadi da dukiyarsa a lokacin yana yaronsa, inda ya hada baki da wasu kamfanoni da suke huldar kasuwanci suka rike masa miliyoyin Naira.
Lauyan wanda ake tuhuma, Barista A. A. Malami (SAN) ya nemi mai karar da ya sake gabatar da shaidunsa na hudu da na shida don ya kara yi musu tambayoyi, bukatar da lauyan mai kara Barista Mohammad Sani ya ki amicewa da ita.
Bayan musayar yawu a tsakaninsu, a karshe lauyan wanda ake kara ya nemi kotun ta ba bangarorin biyu damar yin sulhu a wajen kotu, inda nan take kotun ta amince da wannan bukata.
Alkalin Kotun, Mai shari’a Hadiza dahiru Mustapha ta dage shari’ar zuwa ranar 12 ga Agusta 2014.
Idan za a iya tunawa a kwanakin baya ne dan majalisar, wanda yaro ne ga Alhaji Aminu ya garzaya Babbar Kotun Jihar da ke Bichi don daukaka kara bisa cewar kotun majistaren ba za ta yi masa adalci ba, inda waccan kotun ta kori karar tare da mayar da shari’ar ga kotun majistaren.