Ana zargin dan sanda da karbar hanci daga wanda aka yi wa ’yarsa fyade

Hukumomin ’yan sanda a Jihar Kano suna tuhumar wani dan sanda da aka sakaya sunansa bisa zargin karbar hanci daga hannun wanda ya kai kukan an yi wa ’yarsa fyade.Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ASP Magaji Musa Majiya wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce tuni aka fara gudanar da bincike har ma […]

Ana zargin dan sanda da karbar hanci daga wanda aka yi wa ’yarsa fyade
Ana zargin dan sanda da karbar hanci daga wanda aka yi wa ’yarsa fyade

Hukumomin ’yan sanda a Jihar Kano suna tuhumar wani dan sanda da aka sakaya sunansa bisa zargin karbar hanci daga hannun wanda ya kai kukan an yi wa ’yarsa fyade.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ASP Magaji Musa Majiya wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce tuni aka fara gudanar da bincike har ma an gurafanar da dan sandan da ake zargi a gaban kotun cikin gida na rundunar, kuma idan aka same shi da laifi za azartar masa da hukuncin da ya dace.
“Kasancewar Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya bai lamunci da cin hanci ba, tuni Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano ya bayar da umarnin tsare wanda ake zargi tare gudanar da bincike har an fara gurfanar da dan sandan a kotun cikin gida. Kuma idan aka same shi da laifi za a zartar masa da hukunci daidai da laifin da ya aikata,” inji Majiya.
An ce dan sandan ya karbi Naira dubu daya a matsayin cin hanci daga hannun mahaifin yariya ’yar shekara biyar da ake zargin wani makwabcinsu ya yi mata fyade.
dan sandan mai mukamin saja yana aiki ne a ofishin ’yan sanda na Sabon Gari kuma ana zargin ya karbi na goro ne daga hannun mahaifin yarinyar lokacin da Hukumar Hisba ta mayar da batun fyaden ga ofishinsu inda a nan aka fara kai rahoton faruwar lamarin.
Da yake yi wa Aminiya karin haske, mahaifin yarinyar Malam Garba Ibrahim ya ce dan sandan ya nemi ya ba shi kudi a lokacin da ya kai karar makwabcinsa mai suna Tanimu Ibrahim da ake zargi da yi wa ’yarsa fyade. “A ranar Litinin da ta gabata na kai karar makwabcina kan ya yi wa ’yata fyade, sai wannan dan sanda saja ya nemi na shi Naira dubu daya a matsyain kudin fayil da za a rubuta bayanina. Bayan na biya kudin sai na rubuta maganganuna.”
Ya kara da cewa “Da zan tafi sai ya ce na je na ga wata ’yar sanda mace, ita kuma ta ce kada na damu abin da kawai nake bukata shi ne na ba su hadin kai. Sai kuma wani saja ya ce sai na kawo Naira dubu biyar. Da na tambaya me za a yi da kudin, sai ya ce wai zan sani idan aka kai wanda ake zargin kotu. A nan na sanar da su ba ni da wannan kudin sai dai zuwa gobe (Talata),” inji shi.