Ana zargin Darakta da wasu mutum 2 da yi wa yarinya ciki a Sakkwato

Ana zargin wani magidanci da karbar Naira dubu 50 daga wadanda ake zargi da yi wa ‘yarsa ciki a jihar Sakkwato. Wadanda ake zargin Daraktan Kudi na jihar Ahmad Yahaya Nawawi, da Habibu Abubakar da wani mutum na daban da dukkansu ke aiki a Hukumar Tsara Birane an ce sun yi watanda da yarinyar ce […]

Ana zargin Darakta da wasu mutum 2 da yi wa yarinya ciki a Sakkwato

Ana zargin wani magidanci da karbar Naira dubu 50 daga wadanda ake zargi da yi wa ‘yarsa ciki a jihar Sakkwato.

Wadanda ake zargin Daraktan Kudi na jihar Ahmad Yahaya Nawawi, da Habibu Abubakar da wani mutum na daban da dukkansu ke aiki a Hukumar Tsara Birane an ce sun yi watanda da yarinyar ce ‘yar kimanin shekara 14 mai sayar da ruwan leda, a ofishin daya daga cikinsu abin da ya haifar da shigar cikin da ya kai shiga wata na shida a yanzu.

An ce wadanda ake zargi sun amsa laifinsu a ofishin Hukumar Kiyaye Safarar Mutane da Sauran Laifuffuka (NAPTIP) na yankin.

Daya daga cikin wadanda ake tuhuma, Nawawi, ya shaidawa wakilinmu cewa kage ne kawai aka kitsa musu mai cike da siyasa.

Shi ma Abubakar, ya yi watsi da lamarin inda ya ce amsawarsu ya biyo bayan matsantawa ne kawai da aka yi masu.

Daya daga cikin dangin yarinyar mai suna Hajiya Maryam Yusuf, ta yi zargin an bai wa mahaifin yarinyar toshiyar baki na Naira dubu 250 don ya janye karar inda take zargin tuni ma har ya yi amfani da wani sashi na kudin wajen sayen fuloti.

Sai dai mahaifin yarinyar mai suna Mallam Muhammadu, wanda tunda farko ya karyata batun amsar wasu kudade kan lamarin, ya shaidawa wakilinmu daga baya cewa, ya amshi Naira dubu 50 daga wajen wadanda ake tuhuma yayin da ya yi rashin lafiya.

Ya ce, ya janye karar ne kawai saboda wasu dalilai da kuma yarda da kaddara mai kyau ko marar kyau a matsayinsa na musulmi.

Mahaifin ya kara da cewa, wadanda ake zargi sun yi masa alkawarin kula da yarinyar da kuma daukar nauyin karatunta, amma basu da wani alhaki kan abin da zata haifa. ‘Yar uwar mahaifiyar yarinyar ta shaidawa wakilinmu cewa, mahaifin yarinyar sun rabu da mahaifiyarta wacce ta ke kanwa ce a wajenta tun tana dauke da cikin yarinyar ne, inda ta haife ta a gidanta. “Kuma bata dade da haihuwarta ba ta rasu ta barta saboda jinin da ta zubar yayin nakudarta.” In ji ta.

“Na so a ce yarinyar ta zauna a wajena tunda farko amma mahaifinta ya ki yarda. Tun daga lokacin yarinyar take ta zarya tsakanin gidan mahaifinta da na kakanninta. Idan ka ganta a gidana to tazo neman wani abu ne.”

Ta ce, tana kasar Nijar wajen harkokin kasuwancinta aka kira ta a waya aka shaida mata wannan mummunan labarin, inda tayi maza ta dawo gida.

“Bayan dawowarmu ne muka zarce gidan mahaifinta wanda kuma ya tabbatar mana da faruwar lamarin kuma ya bukaci da kada mu damu domin sun kashe maganar inda ni kuma nan take naki yarda. Da kanshi ya tabbatar mana da cewa, an bashi isassun kuxi don ya zubar da cikin ya kuma ci gaba da daukar dawainiyar yarinyar.”

Ta ce, daga nan ne ta wuce zuwa ofishin NAPTIP inda ta ga yarinyar, sannan ta kara da bayyana cewa, rayuwarta na cikin hatsari saboda rashin mika wuya da ba ta yi ba kan ganin sai an bi wa yarinya hakkinta.

“Maganar gaskiya fa ni ba zan bar lamarin nan ya tafi a banza ba. Sun kira ni sun bani wasu kudade amma na ki karba shi ne yanzu kuma suke min barazana da rayuwata.” Inji ta, inda ta sha alwashin ba zata janye ba har sai taga an yi wa yarinyar adalci.

Kwamandan shiyya na NAPTIP, Abubakar Tabra, wanda ya ki yarda ya yi dogon sharhi, amma ya tabbatar cewa yarinyar tana wajensu, sai dai a cewarsa, bai da damar zantawa da ‘yan jarida a kan lamarin. Sannan ya ki amincewa wakilinmu damar ganawa da yarinyar.

Yayin da wakilinmu ya tuntubi mai bai wa gwaman jihar Sakkwato shawara kan hukumomi, Sidi Aliyu Lamido ya ce suna da masaniya kan lamarin kuma kasantuwar lamarin ya shafi mutane biyu da ke aiki a ma’aikatar kudi tuni sun rubutawa ma’aikatar takarda don daukar matakin da ya dace.

Shi kuma kodinetan Hukumar Kare Hakkin Bil Adama ta ‘Human Rights Commission,’ Lauya Hamza Liman ya sha alwashin bin diddigin lamarin.

A-Kurkura: Guba ko Magani?

Tsohon Shugaban Jami’ar Ilori, Farfesa Ambali ya rasu

ICPC ta hana El-Rufai ganin likita —Hadiminsa

Hanyoyin zuwa Katsina sun zama tarkon mutuwa