Ana zargin DPO da hannu a kisan malamar Islamiyya

Ta bayyana cewa, DPO din ne da kansa ya kai Malama Ummulkhairi waje, duk  cewa ta gargade shi cewa rayuwar marigayiyar na cikin hadari.

Ana zargin DPO da hannu a kisan malamar Islamiyya

Malam Ummulkhair da mijinta

Surukar malamar Islamiyyar nan da aka yi wa kisan gilla bisa zargin satar yara a garin Maraban Jos da ke Jihar Kaduna, ta yi zargin cewa Bature ’Yan Sanda (DPO) na yankin ne ya mika marigayiyar ga  wadanda suka kashe ta. 

Aminiya ta ruwaito cewa wasu futatattun mutane sun yi wa Malama Ummulkhair mai ’ya’ya hudu tare da kona gawarta bayan wasu sun yi mata ihun barauniyar yara a lokacin da take tambayar wasu yara kwatance wurin taron wa’azi a yankin na Maraban Jos da ke Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna.

’Yar uwar mijinta mai suna Zainab Aliyu, ta ce tana tare da Malama Ummulkhair a cikin ofishin ’yan sanda a lokacin da hayaniya ya barke a wajen ofishin ’yan sandan kan zargin marigayiyar.

Ta bayyana cewa, DPO din ne da kansa ya kai Malama Ummulkhairi waje, duk  cewa ta gargade shi cewa rayuwar marigayiyar na cikin hadari.

Zainab ta ce tun da farko, “Muna tare da ita a cikin ofishin. Mutane na ta jifan ’yan sanda da duwatsu su kuma suna harba tiyagas.

“Das DPO ya shigo sai ya ce ina wadda ake zargin. Sai na nuna ta. Shi ne ya kama hannunta ya fara tafiya da ita. Da ya je kusa da kofar fita, sai na ce wa DPO mutanen za su iya kashe ta, idan ya kai ta waje.

“Sai wani dan sanda ya ture ni. Da suka fita waje, sai na bi su zuwa gefen hanya ina kokarin jawo ta, saboda mutane sun fara dukan ta. Sai dan sandan ya jawo ni zuwa cikin station ya ce min in bar su, idan ba haka ba, ni ma za su kashe ni ni ma,” in ji ta.

 

Yadda aka kashe malama a hanyar zuwa wa’azi

Mummunan lamarin ya samu asali ne bayan da Malama Ummulkhairi mai ’ya’ya hudu ta tambayi wasu kananan yara kwatance, a lokacin da take hanyarta ta zuwa wani taron wa’azi a ranar Lahadi a yankin.

Ana cikin haka ne wasu mazauna yankin suka zarge ta da yunkurin satar yara, wanda ya sa cikin dan kankanin lokaci mutane suka yi taron dango tare da far mata, kafin daga bisani jami’an tsaro su je su kwace ta tare da ba ta kariya a ofishin ’yan sanda mafi kusa a yankin.

Daga bisani daruruwan fusatattun matasa da mazauna yankin suka mamaye ofishin ’yan sandan tare da neman a mika musu ita. Duk da kokarin da ’yan sanda suka yi na ba ta kariya da tabbatar da doka da oda, gungun mutanen sun rinjayi jami’an, suka kashe ta, tare da kona gawarta.

Shaidu sun ce duk da harbin gargadji da jami’an suka yi domin razama mutane, abin ya gagara. Wani ganau ya ce, harbin ta samu wani matashi a yayin da wasu da dama suka jikkata a yayin hatsaniyar da ta barke a yankin.

A yayin ziyarar da wakilinmu ya kai yankin Maraban Jos, ya iske an girke motocin jami’an tsaro a gaban ofishin ’yan sandan a yayin da sojoji ke taimakawa wajen gudanar da sintiri.

Wani mazaunin yankin ya danganta abin da ya faru da yawaitar matsalar sace kananan yara a yankin.

“Wannan abin damuwa ne sosai a ce daga zargi kawai za a yi irin wannan danyen aiki. An ce tana hanyar zuwa wani taron lacca na addinin ne lokacin da aka zarge ta. Duk da cewa an kai ta ofishin ’yan sanda amma duk da haka mutane suke je can suka kona ta,” in ji wani mazaunin garin.

 

Ainihin abin da ya faru — Mai unguwa

Mai Unguwar Sabuwar Maraban Jos, Suleiman Isa, wanda da shi aka yi kokarin ceton rayuwar Malama Ummulkhair ya shaida wa wakilinmu cewa mijin marigayiyar ne ya fara kiran shi domin neman ya sa baki.

Ya ce, “Mijin matar, wanda kuma aboki ne, shi ne ya kira ni a waya yake gaya min abin da ke faruwa, cewa mutane sun zarge ta da yunkurin satar yara a hanyarta ta zuwa taron wa’azi wata makarantar Islamiyya,” inda nan take ya hau babur dinsa zuwa wurin tare da kira ya sanar da ’yan sanda.

“Na samu na isa wurin da ake tsare da ita, muka kira ’yan sanda saboda mutanen da suka taru suna da yawa. Da ’yan sanda suka iso, sai muka samu aka kai ta ofishinsu,” in ji mai unguwar.

Ya bayyana cewa a lokacin, Malama Ummulkhair ta roƙe shi ya samo mata ruwa, amma bai iya ba saboda rikicin da ake ciki.

Ya ce duk ƙoƙarin da shi da malamin makantar marigayiyar suka yi wajen rokon mutanen cewa su bar doka ta yi aikinta, ya ci tura.

“Muna wurin tare da malamin makarantarsu, wanda shi  ma ya je caji ofis din, muna roƙon jama’a da kuma bayyana musu cewa ba barauniyar yara ba ce, amma mutane suka ƙi sauraro.

“Daga baya na koma cikin ofishin ’yan sanda ta ƙofar baya inda take zaune, amma ban same ta ba. Lokacin da na sake fitowa, sai na tarar an kashe ta,” in ji hakimin.

Ya bayyana damuwa kan batun ɓacewar yara a yankin, amma ya yi tir da ɗaukar doka a hannu.

Malamin addinin Musulunci da limamin da ya koyar da marigayiywar, Malam Umar Yusuf, wanda aka ƙone babur ɗinsa yayin da yake ƙoƙarin ceto ta daga hannun taron jama’a.

Ya ce: “An taɓa samun matsalar ɓacewar yara a yankinmu. Har yanzu, yaran abokina da suka ɓace ba a gan su ba. Wannan ne ya sa mutane suka yi irin wannan martani. Amma ɗaukar doka a hannu ba daidai ba ne,” in ji shi.

 

Ganawarmu ta karshe da ita — Mijinta

Malam Aliyu Mohammed, wanda shi ne mijin marigayiya Malama Ummulkhair, ya bayyana matukar kaduwarsa ta kisan gilla da aka yi mata, tare da neman a bi masa hakkin jininta.

Ya bayyana cewa ganawarsu da ita ta karshe, ta shaida masa cewa za ta tafi makaranta, har “Na yi mata addu’a Allah Ya dawo da ku lafiya.”

Malam Aliyu ya kara da cewa yana wurin aiki aka kira shi a waya cewa an kama matarsa bisa zargin tana yunkurin garkuwa da yara.

“Shi ne na kira abokina, na ce ya je wurin kafin in karaso. Ko da na isa wurin sun riga sun kona gawarta,” in ji shi.

“Wannan lamari ya girgiza ni, saboda babu laifin da ta yi. Malamar makarantar Islamiyya ce kuma tana hanyar zuwa taron wa’azi ne, mutane suka tare ta suna zargin ta da satar yara,” in ji shi.

Ya bayyana ta a matsayin mace mai son zaman lafiya da kuma tsoron Allah, sannan ya roƙi hukumomin gwamnati su yi adalci su kwato hakkin jininta.

Ya ce, yanzu da rasuwarta shi kadai ne zai kula da ’ya’yansu hudu da ta bari. “Duk lokacin da na kalle su, sai na fashe da kuka. Jiya da dare, ƙaramin ɗanmu mai shekara huɗu, ya yana ta tambaya me ya sa mahaifiyarsa ba ta dawo gida ba, sai dai na yi ƙoƙarin rarrashinsa,” in ji shi.

“An yi mata ƙarya aka zarge ta, sannan aka kashe ta, aka bar ni kaɗai tare da ’ya’yanmu. Abin da nake so shi ne adalci daga gwamnati saboda talaka ne ni,” in ji shi.

 

Amnesty International ta nemi a gudanar da bincike

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta tir tir da kisan gillar tare da kira da a gudanar da bincike mai zurfi a kansa.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook, kungiyar ta ce: Kungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International ta yi Allah wadai da abin da ta kira mummunan kisan gilla da jama’a suka aikata, tare da neman cikakken bincike.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook, kungiyar ta ce: “Amnesty International na yin Allah wadai da mummunan kisan Malama Ummulkhairi, mahaifiyar yara biyar, a Maraban Jos da ke kan titin Kaduna-Zariya.”

Kungiyar ta kuma bukaci a binciki zargin cewa jami’an ’yan sanda ne suka ta ga taron jama’a da suka halaka ta.

Kwamishiniyar Harkokin Mata da Ci-gaban Al’umma ta Jihar Kaduna, Hajiya Rabi Salisu, ta ziyarci iyalan marigayiyar Malama Ummulkhairi tare da tabbatar musu cewa za a yi adalci.

Ta ce: “Muna roƙon ku da ku yi haƙuri ku ci gaba da yi mata addu’a. Mun tabbatar cewa zargin da aka yi mata ƙarya ne, amma wasu miyagun mutane ne suka aikata wannan aiki. Da yardar Allah za a yi adalci.”

Lauya ya kai kara ga Sufeto-Janar na ’Yan Sanda

Lauya kuma mai fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam, Hamza N. Dantani, ya aika da takardar ƙorafi ga Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Nijeriya yana neman bincike mai zaman kansa kan zargin cewa jami’an ’yan sanda sun miƙa marigayiyar ga taron jama’a da suka kashe ta.

Ya bayyana hakan a matsayin yiwuwar take haƙƙin kundin tsarin mulki da kuma gazawar jami’an tsaro wajen kare rayuwar wanda ke hannunsu.

Wani masanin tsaro, Mohammed Ali, ya ce yawaitar irin waɗannan kisan gilla na faruwa ne saboda rashin hukunta masu laifi. “Duk wanda aka gani a bidiyo ko kuma shaidu suka tabbatar ya shiga cikin kisan, dole a gurfanar da shi bisa tuhumar sa da aikata manyan laifuka, kuma idan aka same shi da laifi a aiwatar da hukuncin da kotu ta yanke domin ya zama izina ga wasu,” in ji Mohammed Ali.

Mutum 80 sun shiga hannu — ’Yan sanda

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta ce ta kama sama da mutum 80 da ake zargi da hannu a kisan.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, DSP Mansur Hassan, ya shaida wa wakilinmu cewa ana ci gaba da kama wadanda ake zargi.

“Mun kama sama da mutum 80. Suna hannunmu yanzu, kuma muna yin duk mai yiwuwa domin gudanar da cikakken bincike. Duk wanda aka samu da laifi za a hukunta shi bisa doka,” in ji shi.

Ya ce bincike ya nuna cewa an yi wa marigayiyar zargin ƙarya. Kuma masu zanga-zangar sun toshe manyan hanyoyin da ke kaiwa ofishin ’yan sanda, lamarin da ya hana jami’an ƙarin ɗauki isa da wuri.

Ya jaddada cewa jami’an sun yi aikinsu yadda ya kamata duk da ƙalubalen da suka fuskanta, tare da alƙawarin cewa duk masu hannu a kisan za su fuskanci hukunci.

“Rundunar ba za ta amince da irin wannan ɗabi’a ba, kuma duk wanda aka kama zai fuskanci hukuncin doka,” in ji shi.