Ana zargin Fasto da yi wa ’yarsa fyade a Kuros Riba
’Yan sanda a Jihar Kuros Riba sun kama Shugaban Majami’ar Zion Church da ke Kalaba, Fasto Daniel Asuguo Udoh, bisa tuhumarsa da yi wa ’yarsa mai suna Rachel Dominic mai shekara takwas da haihuwa fyade. […]
’Yan sanda a Jihar Kuros Riba sun kama Shugaban Majami’ar Zion Church da ke Kalaba, Fasto Daniel Asuguo Udoh, bisa tuhumarsa da yi wa ’yarsa mai suna Rachel Dominic mai shekara takwas da haihuwa fyade. Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Hafiz Muhammad Inuwa ne ya gabatar da Faston tare da sauran mutum 80 da ’yan sanda suka kama kan zargin aikata laifuffuka daban ga ’yan jarida a Kalaba. Faston ya shaida wa Aminiya cewa “Ba yin kaina ba ne, Shaidan ne. Ni ma ban san yadda aka yi ba na aikata haka.” Tun farko da yake gabatar da wadanda ake zargin Kwamishina ’Yan sanda Hafiz Inuwa ya ce ana zarginsu da aikata miyaguan laifuffuka da suka hada da fashi da makami da zamba cikin aminci da ayyukan kungiyar asiri. Hafiz Muhammad Inuwa ya ce sakamakon samun bayanan sirri da wadansu ’yan kasa nagari suka rika kai musu ne, suka rika kai samame suna kama wadanda ake zargin.
Kwamishinan ya bayar da bayanin wadanda aka kama da inda aka kama su da irin nau’u’o’in laifuffukan da ake zarginsu da aikatawa. Ya ce “Hukumar ’yan sanda a Jihar Kuros Riba a karkashin jagorancina, ta yi katarin kama wadanda ake zarginsu da aikata miyagun dabi’u daban-daban har su 80.”
Da ya juya kan ma’auratan da aka kama bisa zargin jinginar da dansu a makon jiya kuwa, ya ce magidancin ya shaida musu cewa saboda ana bin sa bashin Naira dubu 120 shi da matarsa sun yanke shawarar su sayar da dansu mai shekara biyu. Kuma bayan sun yi haka ne sai matar tasa ta garzayo ta sanar da ’yan sanda.
Da Aminiya ta tambayi wanda ake zargin mai suna Daniel Bassey kan abin da ya yi zafi har ya kai su ga yanke wannan muguwar shawara ta jinginar da dansu, sai ya ce “Bashi ake bi na har Naira dubu 120, na kasa biya. Mai kudin ya dame ni, kuma muka yanke shawarar mu jinginar da dan namu, muka karbi kudin don mu biya bashi. Wannan tsautsayi ne tunda ba ni da wani, wanda zai taimake ni; ga shi mai kudin ya sa ni a gaba,” inji shi.
Daga karshe Kwamishina Hafiz ya gargadi duk wadansu masu aikata ba daidai ba da su shiga taitayinsu, kuma ya ja kunnen ’yan siyasa da su yi hattara, su kiyayi haddasa rikici a lokutan yawon neman magoya bayansu.