Ana zargin kisan kiyashi a Sudan ta Kudu

Rahotanni daga Juba, babban birnin Sudan ta Kudu sun ce dakarun gwamnati sun kashe fiye da ’yan kabilar Nuer 200, bayan da suka tasa keyarsu zuwa wani caji ofis na ’yan sanda.Haka kuma a wasu unguwannin birnin, ’yan bindiga na bi gida-gida suna kashe duk wanda ba dan kabilar Dinka ba ne.Gidan Rediyon BBC Landan […]

Ana zargin kisan kiyashi a Sudan ta Kudu

Mista Salva Kiir Shugaban Sudan ta KuduRahotanni daga Juba, babban birnin Sudan ta Kudu sun ce dakarun gwamnati sun kashe fiye da ’yan kabilar Nuer 200, bayan da suka tasa keyarsu zuwa wani caji ofis na ’yan sanda.
Haka kuma a wasu unguwannin birnin, ’yan bindiga na bi gida-gida suna kashe duk wanda ba dan kabilar Dinka ba ne.
Gidan Rediyon BBC Landan wanda ya ruwaito labarin ya ce kimanin farar hula dubu 45, suka fake a sansanonin Majalisar dinkin Duniya da ke fadin kasar, yayin da fiye da mutum dubu 80, suka kaurace wa gidajensu.
Babban Sakataren Majalisar dinkin Duniya, Mista Ban Ki-moon ya bukaci karin dakarun kiyaye zaman lafiya zuwa dubu 12 a kasar.
Rikici tsakanin dakarun da suke biyayya ga Shugaban kasar Salba Kirr wanda dan kabilar Dinka ne da na tsohon mataimakinsa Riek Machar dan kabilar Nuer ya watsu sassa da dama na kasar, inda kabilun biyu ke kashe junansu.
Gwamnatin Sudan ta Kudu ta musanta cewa tana mara wa rikicin kabilancin baya.
Mahukunta sun ce an kashe mutum 500 a rikicin, sai dai wasu cibiyoyin ba da agaji sun ce adadin yana iya fin haka.
Shugaba Kiir ya ce a shirye yake ya tattauna da Mista Machar – kuma wani aarin wakilan ministocin harkokin kasashen waje na Gabashin Afirka sun ce za su shiga tsakani- amma sai tsohon mataimakinsa zai halarci zaman ba tare da gindaya wani sharadi ba.
Mista Machar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa a shirye yake a tattauna idan za a sake magoya bayansa daga inda ake tsare da su.