Ana zargin kyanwa da yunkurin kashe tsohuwa

’Yan sanda kasar Japan na zargin mage mai garamramba a titi da laifin yunkurin halaka wata tsohuwa ke jinya a gidanta. ’Yar tsohuwa Mayuko Matsumoto ta iske mahaifiyarta jina-jina da yanka 20 a fuskarta ranar Litinin din da ta gabata, a gidanta da ke wani yanki mai tsaunuka a Kudancin kasar Japan. ‘’Yan sanda sun […]

Ana zargin kyanwa da yunkurin kashe tsohuwa

’Yan sanda kasar Japan na zargin mage mai garamramba a titi da laifin yunkurin halaka wata tsohuwa ke jinya a gidanta.

’Yar tsohuwa Mayuko Matsumoto ta iske mahaifiyarta jina-jina da yanka 20 a fuskarta ranar Litinin din da ta gabata, a gidanta da ke wani yanki mai tsaunuka a Kudancin kasar Japan.

‘’Yan sanda sun kaddamar da binciken yunkurin kisa bayan da suka ga raunukan, inda wadansun su sun yi matukar muni, kamar yadda mai gabatar shirin rediyo na RKK ya bayyana.

“Da muka ganta kwance cikin jinni, inda ya baibaye habarta. Fuskarta jike take da jini. Ni ban san abin da ya faru ba,” a cewar ’yar Matsumoto kamar yadda ta bayyana wa gidan rediyon RKK.

Matsumoto dattijuwa mai shekara 82 an ruwaito cewa ba ta iya yin magana, kuma dole aka ba ta kulawar gaugawa, kamar yadda kafar labarai ta Kyodo ta bayyana.

Binciken da aka gudanar ya nuna babu alamar da ke nuna cewa mutane sun sshiga cikin gida, ko sun fita daga ciki a lokacin da aka kai mata farmakin, kamar yadda wani gidan talabijin mai zaman kansa na NTb ya nuna.

Daga bisani sun yi has ashen cewa raunukan Matsumoto sun yi kama da na yakushin mage, kamar yadda suka bayyana.

Don haka ’yan sandan sun mayar da hankalinsu kan magunan da ke gararamba a kewayen gidan Matsumoto, inda suka ga dishi-disshin jini a jikin dayarsu, kamar yadda jaridar Nishinippon Shimbun ta ruwaito a ranar Juma’ar da ta gabata.

’Yan sandan na gudanar da bincike kan samfurrin jinin da suka dauka daga gashin kirjin kyanwar, wanda aka yi has ashen ya fallatsa ne daga yakushin da ta yi wa tsohuwar,” kamar yadda mai watsa shiryee-shirye a kafar labarai ta NHK ya bayar da rahoto.

Sai dai mai magana da yawun ‘

’Yan sanda ya ki yin sharhi kan matsalar da aka bijiro musu da ita ranar Juma’a, amma ya sanar da Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa masu bincike ba su karyata abin da kafafen yada labarai suka ruwaito ba.