Ana zargin likita da kisan jaririya a Kano
Iyalai da ’yan uwan Malam Idris Zubairu mazaunin garin Yandadi da ke karamar Hukumar kunci, Jihar Kano sun nemi mahukunta da su bi musu hakkinsu a kan wani likita sakamakon yin sanadin mutuwar ’yar jaririyar da aka haifa musu makonni biyu da suka gabata. Aminiya ta kalato cewa a Juma’ar da nakuda ta kama uwargidan […]

Iyalai da ’yan uwan Malam Idris Zubairu mazaunin garin Yandadi da ke karamar Hukumar kunci, Jihar Kano sun nemi mahukunta da su bi musu hakkinsu a kan wani likita sakamakon yin sanadin mutuwar ’yar jaririyar da aka haifa musu makonni biyu da suka gabata.
Aminiya ta kalato cewa a Juma’ar da nakuda ta kama uwargidan Malam Idris mai suna Hafsa, sai mijinta ya nemi taimakon makwabcinsa mai suna Abdussalam Ya’u wanda likita ne, sai dai a wannan taimako ya janyo sanadiyyar mutuwar jaririyar, sakamakon yankanta da likitan ya yi a wurare uku a kanta, baya ga haddasa wa mai jegon kamuwa da cutar da ake zato za ta iya zama yoyon fitsari.
A yanzu haka maijego Hafsa na can kwance a asibitin garin Bichi, inda ake kokarin yi mata aiki a karo na uku sakamakon raunukan da ta samu a lokacin da likitan ke kokarin fito mata da jaririyar tata daga cikinta.
Malam Idris Zubairu ya shaida wa Aminiya yadda lamarin ya faru cewa ya tafi nemo mota don kai matarsa asibiti sai wannan likita ya yi wa matarsa aikin. “Da farko da ya duba ta ya ce haihuwa za ta yi amma tana da wata matsalala a gabanta don haka ya umurce ni da in je in samo mota don kai ta asibiti. To bayan na tafi nemo mota ne sai na zo na iske cewa likitan ya yi mata aiki har ya fito mata da jaririyarta, wacce ta riga ta rasu. Sai dai da na duba yarinyar sai na ga akwai yanka a kanta har guda uku. Daga nan sai na dauki matata na kai asibitin ’Yandadi, inda aka yi mata dinki a gabanta tare da rubuta mata magunguna. Bayan kwana uku sai dinki ya bude, haka na mayar da ita asibitin, a nan ma aka sake yi mata dinki a wurin Shi ma an yi kwana uku sai ya bude. Daga nan suka yi uamrnin na kai ta asibitin garin Bichi, inda suka yi mata aiki,” inji shi.
Malam Idris ya kara da cewa: “Ana cikin wanann hali sai maganar ta wastu a cikin garin nan, don haka Dagaci ya dauke ni ya kai ni wurin Hakimi daga nan kuma muka je gaban sarki inda bayan Sarkin Kano ya ji wannan magana, a take ya bayar da umarnin kama makwabcin nawa.”
Har ila yau Malam Idirs ya bayyana cewa yana neman Abdussalam ya kula da dawainiyar matarsa har ta sami lafiya sannan batun ’yarsa kuma kamar yadda kowa ya sani hakkin rai yana kan wanda ya yi sanadin salwantarsa.
A nasa bangaren, wanda ake zargin ya shaida wa Aminiya cewa tsautsayi ne ya jawo faruwar lamarin kasancewar sun dade suna harkokin abin da ya shafi kula da lafiya da makwabcin nasa.
Likita Abdussalami wanda ya ce ba ya aiki a kowane irin asibiti sai dai yana yin aiki a matsayin taimakon al’umma: “Kin san idan mutum yana da lasisin likitanci zai iya aiki a asibiti haka kuma zai iya yi a cikin gidaje don taimakon al’umma. Kusan duk a yankin ina taimakonsu ta harkar abin da ya shafi lafiyarsu da ta iyalansu, domin ko shi Malam Idirsi mun jima ina kula da lafiyar iyalansa.”
Likita Idirs ya kara da cewa: “Lokacin da na duba wannan mata sai na ga ta kusa haihuwa, amma kuma ba za ta iya haihuwa ba kasancewar wurin da jaririn zai fito yana da kankanta. Hakan ya sa na nemi ya kai ta asibiti, sai dai bayan ya fita sai na ga cewar haihuwar tana dada matsowa, ma’ana jaririyar da ke cikinta tana ta yunkurin fitowa ga shi babu hanya isasshiya. Sanin hatsarin da matar ke ciki na yiyuwar kamuwa da cutar yoyon fitsari ko rasa jaririyar sai na yi mata abin da ake kira kari da Hausa, a maimakon a bar wurin ya yage da kansa wanda zai iya haifar da matsala. Bayan na yanka ta sai aka sami jaririyar ta fito sai dai an sami akasi, domin igiyar mahaifa ta nade mata wuya har sau uku. Wannan ne ya yi sanadiyyar mutuwar jaririyar. Kasancewar ba ni da isassun kayan aiki sai na umarci makwabcin nawa da ya dau mai jegon ya kai ta asibitin Bichi ko na Kazaure don yi mata dinki. Nan na rubuta takarda da ke dauke da bayanin dukkanin abubuwan da na yi wajen karbar haihuwar. Amma maimakon ya tafi asibitin da na gaya masa sai ya je na cikin kauyenmu, inda aka samu matar da ke aiki ba ta karanci wani abu na harkar lafiya ba illa harkar koyarwa. A nan dai ta lallaba ta yi mata dinki, wanda ya bude, sannan suka sake mayar da ita aka sake yi mata wani dinkin shi ma ya farke.”
A cewar Likitan, bayan lamarin ya faru sai aka zuga Malam Idiris ya kai kara ofishin ’yan sanda, kafin daga bisani ya sa hannu a kan takarda cewa ya yafe dukkanin abin da ya faru.
Har ila yau likita Abdussalam ya zargi Dagacin garin ’Yandadi da rura wutar lamarin, sakamakon bambancin akida da suke da ita a tsakaninsu. “Da ma akwai rashin jituwa tsakanina da maigarinmu saboda bambancin akida da muke da ita, ni dan Izala ne shi kuma dan darika ne. A lokuta daban-daban ya kai ni wurin ’yan sanda cewa ni dan Boko Haram ne, inda har ya jawo aka hana mu gina masallaci a garin. A wani lokaci ma sai da ya nemi masu gidan hayar da nake ciki su kore ni don dai ya ga bayana. A yanzu haka shi ya rura wutar wannan rigima domin kamar yadda na yi maki bayani, a gaban ’yan sanda makwabcin nawa ya sa hannu cewa ya yafe maganar sai kuma yanzu ga shi ana kokarin kama ni.”
DSP Magaji Musa Majiya shi ne kakakin rundunar ’yan sanda a Jihar Kano. Ya tababtar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa tuni rundunarsu ta kama likitan da ake zargi da aikata wanann danyen, aiki wanda a yanzu haka batun yana gaban sashen binciken manyan laifuffuka na rundunar. Ya ce da zarar sun kammala gudanar da bincike, za su gurfanar da wanda ake zargi gaban kotu.