Ana zargin likitan El-Rufai da bayar da rahoton jinya na bogi
Ana zargin likitan ya bayar da bayanai na bogi domin tallafa wa buƙatar belin El-Rufai a wata shari’a.
Likitan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shiga tsaka mai wuya yayin da yake fuskantar bincike daga ƙungiyar da ke sa ido kan harkokin likitanci a Najeriya MDCAN.
Lamarin na zuwa ne bayan Hukumar Yaƙi da Rashawa ICPC ta gurfanar da shi a kotu kan zargin bayar da rahoton jinyar tsohon gwamnan na bogi.
- Shugaban Senegal ya zama sabon shugaban ECOWAS
- HOTUNA: An kama mutane 6 masu yi wa ’yan ta’adda safarar kayan masarufi a Borno
A cewar ICPC, ana tuhumar Dokta Bello Abubakar da laifuka huɗu, ciki har da zargin bai wa jami’an gwamnati bayanan ƙarya da kuma amfani da wani rahoton jinya da ake zargin bai samu amincewar Asibitin Ƙasa da ke Abuja ba, domin tallafa wa buƙatar belin El-Rufai a wata shari’a.
Majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa kafin gurfanar da likitan, ICPC ta ce ta nemi ƙwararrun likitoci a Najeriya da Amurka su tantance rahoton, inda suka bayyana cewa bai inganta ba.
Sai dai har yanzu kotu ba ta yanke hukunci kan zarge-zargen ba.
Takardun kotu sun kuma nuna cewa Babban Daraktan Kula da Lafiya na Asibitin Ƙasa ana sa ran zai bayar da shaida cewa rahoton da ake magana a kai bai samu amincewar asibitin ba, kuma ba a bi ƙa’idojin da suka dace wajen fitar da shi.