Ana zargin ma’aikacin Hukumar Raya Birnin Dutse da sace taranfomarta
Ana zargin wani ma’aikacin Hukumar Tsara Birnin Dutse (DCDA) da ke Jihar Jigawa mai suna Malam dalha Isah da sace wata na’urar aransfoma ta hukumar tare da saar da ita Naira dubu biyar.Ma’aikacin da ake danganta shi da Masarautar Dutse kuma aka fi saninsa da Jafanis wata majiya ta ce an kasa hukunta shi saboda […]
Ana zargin wani ma’aikacin Hukumar Tsara Birnin Dutse (DCDA) da ke Jihar Jigawa mai suna Malam dalha Isah da sace wata na’urar aransfoma ta hukumar tare da saar da ita Naira dubu biyar.
Ma’aikacin da ake danganta shi da Masarautar Dutse kuma aka fi saninsa da Jafanis wata majiya ta ce an kasa hukunta shi saboda dangantakarsa da fada.
Shugaban Hukumar DCDA, Alhaji Bashir Aminu Dutse wanda basarake ne a masaruar ya ce suna da masaniya kan faruwar lamarin kuma wanda ake zargin ba ya da wata alaka da Masarautar Dutse kuma karamin ma’aikacine da tuni ya ba da umarnin a ba shi takardar tuhuma, sai dai ya ki amsawa saboda haka suka sanar da Shugaban Ma’aikata na Jihar Alhaji Mustapha Aminu wanda ya ce a ba shi takardar gargadi bayan haka a mika batun ga ’yan sanda domin su kama shi kuma su tuhume shi a kan lamarin domin bincikar yadda lamarin ya kasance.
Shugaban Hukumar ya gaya wa manema labarai cewa Isah ne ya dauki takardar hukumar ya sanya sunayen shugabanninta ya sanya hannunsu, ya yi takardar jabu ya kai wa Shugaban karamar Hukumar Dutse kan ya sayi taransfomar a matsayin gwanjo a kan Naira dubu biyar.
Wata majiya ta yyi zargin cewa da sa hannun wasu daga cikin shugabanin Hukumar DCDA a badakalar da ake tuhumar wancan karamin ma’aikaci amma saboda wasu ba su amfana da badakalar ba ce, sai suka tona asiri.
Lokacin da wakilinmu ya tuntubi Shugaban karamar Hukumar Dutse Alhaji Abdulaziz dan Kofa kan labarin da ya cika gari cewa ya sayi kayan sata, sai ya ce ba ya da masaniya kan batun ballantana ya yi magana da manema labarai, don haka ba zai ce komai ba.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa ASP Abdu Jinjiri ya ce, lamarin bai iso gare su ba, kuma duk lokacin da ya iso za su shaida wa manema labarai.