Ana zargin magidanci da yi wa saurayi fyade

A ranar Asabar da ta gabata ce wani matashi mai suna Kabiru Baffa mai shekara 25 da ke Unguwar Malali, Kaduna ya zargi wani magidanci, Alhaji Abubakar Abudullahi da yi masa fyade a lokacin da ya je gidansa domin karbar yadin shadda.Lamarin ya faru ne a Unguwar Badarawa Kwaru bayan Sallar Magriba, inda wata majiya […]

Ana zargin magidanci da yi wa saurayi fyade
Ana zargin magidanci da yi wa saurayi fyade

A ranar Asabar da ta gabata ce wani matashi mai suna Kabiru Baffa mai shekara 25 da ke Unguwar Malali, Kaduna ya zargi wani magidanci, Alhaji Abubakar Abudullahi da yi masa fyade a lokacin da ya je gidansa domin karbar yadin shadda.
Lamarin ya faru ne a Unguwar Badarawa Kwaru bayan Sallar Magriba, inda wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa wanda ake zargin, Alhaji Abubakar dan kasuwa ne da ke zuwa Dubai yana sayo shaddodi yana sayarwa, kuma akwai dangantaka mai karfi a tsakaninsa da mahaifiyar Kabiru wanda ya sa Kabirun zuwa gidansa.
Kabiru ya shaida wa Aminiya cewa Alhajin ya ba shi shayi ne ya sha, shayin ya sa barci, kafin ya aikata luwadi da shi.
Ya ce bayan ya farka Alhajin wanda ke kwance a kansa ya dauko wuka ya nuna masa cewa idan har bai bari ya kare lalata da shi ba zai daba masa.
Kabiru ya ce ya ci gaba da yunkurin tashi amma ya kasa, da ma kuma ba ya jin dadin jikinsa kafin ya je gidan. Kuma Kabiru da Alhaji Abubakar sun yi wa kansu jina-jina sakamakon rigimar da suka yi a cikin dakin Alhajin kafin makwabta su shiga tsakaninsu.
“Tunda na taso na san shi tare da mahaifiyata har nake kiransa da Kawu Abu. Na san shi yana sana’ar sayar da shaddodi da yake kawowa daga Dubai. Saboda haka ne sai na fada wa mahaifiyata cewa ta fada masa ina bukatar in sayi shadda a wurinsa. Kwanaki bayan na dawo gida sai na gan su sun fito daga cikin gidanmu da mahaifiyata tana bude masa kofa, daga nan sai na taya ta bude masa kofar. Bayan ya fito sai na wuce wurin mahaifiyata inda ita kuma ta aike ni in dauko mata shadda domin a yi mata bugu,” inji shi.
Ya kara da cewa, “Bayan na fito daga gida ashe bai tafi ba yana waje. Sai ya kira ni ya ce wai lambar wayar da na ba shi kwanaki ta karya ce domin in ya buga ba ya samuna. Sai na fada masa cewa lokacin da na ba shi lambar, wayata ce ta bata. Sai ya karbi wayar da ke hannuna ya sake saka lambarsa a ciki. Sannan ya ce zai kira ni. Bayan awanni sai ya kirani ya ce maganar shaddar ce yake son mu gana a kai. Sai ya bukaci da in je gidansa da ke Layin Zakari a Badarawa Kwaru domin in karba.
Ya ce bayan isarsa gidan sai Alhaji Abu ya ce masa ba ya da kirki domin bai taba zuwa gidansa ba, kuma ya yi masa ta yin abinci, ya ce ya koshi saboda ba ya jin dadin jikinsa. “Sai ya ce ban isa ba, yaya za a yi in zo gidansa ban ci abinci ba. Ba ya da mata shi kadai ne a gidan sai ya zubo min shinkafa. Da na dan ci sai na ce na koshi, sai ya ce in dauki nama in ci.  Kamar minti biyu da cin naman sai na ce ina jin amai. Daga nan ya bude wata kofa a cikin gidan domin in je in yi aman. Bayan na yi sai ya ba ni shayi. Da ya zuba min shayin na fara sha sai ya zo yana yi min wasa. Da fara shan shayin sai na ji ban san inda nake ba. Na tashi ne kawai na ji kamar na zauna a kan wani abu da ke damuna a cikin duwawuna. Da na farka sai na gan ni a kwance rub-da-ciki, kuma na ji mutum a kaina kwance, ya danne hannuwana, ya hada da kaina ya danne. Sai na fara ihu sai ya ce in bari ya fitar da maniyi ko nawa nake so zai ba ni.”
Kabiru ya ce, “Da na ji haka sai na kara ihu, sai na ga ya dauko wuka ya nuna min cewa idan ban yi shiru ba, zai caka min. Daga nan sai ya ajiye wukar yana cewa in yi hakuri in tsaya zai ba ni duk abin da nake so. Da ya ajiye ta sai na kai hannu zan dauke ta sai ya riga ni. Ya rike na rike wajen kaifi, garin ja sai ya yanke min hannu. Daga nan sai ya ajiye wukar yana ba ni hakuri. Da na ga haka sai na sake kai wawura ga wukar. Da na samu na dauke sai na rika caka masa, yana ihu, ban daina ba. Yana ihu, ina ihu. Ina kokarin in fita shi kuma ya danne ni. Daga nan sai ya fara cizona.”
Kabiru ya ce da ya fito daga cikin gidan yana ihu tsirara, yana neman a taimake shi. Shi kuma Alhajin na yi masa ihun barawo, sai mutane suka rike shi. Nan take sai ya nemi a kirawo mahaifiyarsa.
Mahaifiyarsa, Hajiya Fatima Ali ta ce ta yi matukar mamaki da ta ji cewa danta da Abubakar suna kwance a Asibitin Garkuwa suna karbar magani. “Muna da alaka da shi kuma mun dade tare. Domin akwai ’yar yata da ke auren babansa, kuma tun yana karami muke tare. Yana zuwa wurinmu har cikin uwar dakata yake shiga domin kamar da yake a wurinmu,” inji ta.
Ta ce, ana yawan zarginsa da wannan harka, “Duk abubuwan da nake ji dangane da halayensa ina fada wa dana domin ya yi hankali da shi. Kuma dana bai san gidansa ba, shi ya sa da aka kira ni da daddare cewa ga Kabiru da Alhaji Abu a Asibitin Garkuwa sai na yi mamaki,” inji ta.
“Da na je wurin Alhaji Abu a asibiti cewa ya yi ko yana wannan abu, ba zai yi da Kabiru ba. Amma ga abin da Kabiru ya yi masa zai sa makiya su yi mana dariya.” Ya ce wai likita ya ce babu komai a jikin Kabiru amma likitan ya ce zai ba da sakamakon bincikensa. “Abin da ya sa nake son daukar mataki shi ne saboda bayan na ziyarce shi sau biyu a asibiti na ji abin da yake fadi cewa wai Kabiru dan fashi ne ya shigar masa gidan domin ya yi masa sata. Saboda haka nake son fada wa duniya cewa dana ba dan fashi ba ne,” inji ta.
Alhaji Abubakar ya musanta zargin yin lalata da yaron, ya ce “Kabiru ya zo gidana da karfe 8:30 na dare a ranar, ya koma gida saboda mahaifiyarsa ta nemi ya koma. Ya sake dawowa da karfe 11:00 na dare ya kira ni a waya, na tambaye shi ko akwai matsala ce, ashe yana kofar gidana. Bayan na bude masa kofa sai ya shigo. Da shigowarsa sai ya ce in ba shi ruwan zafi domin ya sha shayi. Bayan na ba shi, sai muka zauna domin kallon talabijin. Da ga nan sai na ce zan tafi daki in kwanta. Shi ma ya ce ai a gidana zai kwana. Ganin haka sai na tambaye shi ko mahaifiyarsa ta san zai kwana a wurina sai ya ce eh,” inji shi.
Ya ce bai san daliliin da ya sanya Kabiru ya yi masa haka ba, domin shi ba dan luwadi ba ne kuma koda suka kwana da Kabiru a gado daya bai kusance shi ba.
Alhaji Abubakar ya ce Kabiru na girmama shi, haka mahaifiyarsa saboda haka ne ya umarci likitan da ke kula da shi a asibitin ya gudanar da bincike a duburar Kabiru domin gano gaskiyar zargin da yake masa.
Ya ce ya bukaci a gudanar da bincike kan sauran abincin da Kabirun ya ci da shayin da ya sha domin ya wanke kansa daga zargin da ake yi masa.
Da aka tambaye shi ko zai dauki matakin shari’a a kan Kabiru saboda zarginsa da luwadi sai ya ce bai yi shawarar matakin da zai dauka ba. Sai dai ya bar wa Allah komai.
Alhaji Abubakar da abokin fadarsa Kabiru duk sun samu mumunanan raunuka sakamakon caka wa juna wuka da cizon da suka yi rika yi a yayin fadar da suka yi cikin dare.