Ana zargin magidanci da yi wa ’yarsa fyade

Rundunar ’Yan sandan Jihar Borno ta kama wani magidanci da ake zarginsa da yi wa ’yarsa mai shekara 10 fyade a Unguwar Moduganari da ke cikin birnin Maiduguri.Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Mista Clement Adoda ya bayyana haka a lokacin da ya gabatar da wasu mutanen da aka kama kan zargin aikata laifuffuka daban-daban ga manema […]

Ana zargin magidanci da yi wa ’yarsa fyade
Ana zargin magidanci da yi wa ’yarsa fyade

Rundunar ’Yan sandan Jihar Borno ta kama wani magidanci da ake zarginsa da yi wa ’yarsa mai shekara 10 fyade a Unguwar Moduganari da ke cikin birnin Maiduguri.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Mista Clement Adoda ya bayyana haka a lokacin da ya gabatar da wasu mutanen da aka kama kan zargin aikata laifuffuka daban-daban ga manema labarai a ofishinsa da ke Maiduguri.
Kwamishina Adoda, ya kara da cewa wanda ake zargi da yi wa ’yarsa fyade, mai suna Idris Ali ya amsa laifinsa.
Kuma ya gabatar da wani matashi mai suna Bana Kyari wanda ya fito daga Unguwar Bolori, bisa zarginsa da yi wa wata karamar yarinya ’yar shekara 3 fyade.
Kwamishinan ya kuma bayyana sunan wani matashi mai shekara 22 mai suna Ahmadu Bajoga Bello, wanda ya fito daga kauyen Wuyaku a karamar Hukumar Biu ta Jihar Borno, bisa zargin kashe wani matashi mai suna Abdullahi Sa’idu a kan Naira 200, a shekara ta 2010, inda ya gudu bayan aukuwar haka.
Ya ce an sake kama shi a ranar 31 ga Mayun bana, kuma ya rubuta wata takarda mai nuni da cewa ya aikata wannan laifi.
Kwamishinan ya kuma roki al’umman Jihar Borno su taimaka wa jami’an tsaro ta hanyar bayar da bayanan duk wani abin da ba su amince ba a jihar, ta yadda za a samu nasarar murkushe aikata munanan dabi’u a jihar.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi